Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna Afrika
  • Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi Afrika
  • Maulidin 2026: IMC Ta Yi Kira Da Ƙarfafa Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Najeriya Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Taya Sarkin Musulmi Murnar Cika Shekaru 70, Ya Yi Masa Addu’ar Ƙarin Lafiya Da Tsawon Rai Afrika
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika

Ceferin Ya Ce Ba Zai Yi Takarar Shugabancin FIFA Ba
Published: August 25, 2026 at 12:40 PM | By: Bala Hassan

Ceferin Ya Ce Ba Zai Yi Takarar Shugabancin FIFA Ba, Yayin da Infantino Ke Neman Goyon Bayan Kasashe Masu Karamin Karfi

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai UEFA, Aleksander Čeferin, ya ce ba zai tsaya takarar shugabancin FIFA ba a zaben da ake sa ran gudanarwa a watan Maris na 2027.

Čeferin ya bayyana cewa, duk da cewa yana adawa da wasu matakai da shugaban FIFA, Gianni Infantino, ke dauka, ba shi da niyyar neman maye gurbinsa. Sai dai ya yi hasashen cewa wani dan takara zai fito domin kalubalantar Infantino a zaben.

Čeferin ya kasance daya daga cikin manyan masu sukar Infantino, musamman kan shirin da FIFA ta gabatar na sayar da wani kaso na kudaden kasuwancin gasannin FIFA ga masu zuba jari masu zaman kansu. An yi watsi da shirin ne bayan fuskantar turjiya daga hukumomin kwallon kafa daban-daban.

Shugaban UEFA ya bayyana shirin a matsayin wani abu da ya fi hatsarin da shirin European Super League ya haifar, yana mai cewa matakin zai iya yin illa ga tsarin tafiyar da kwallon kafa na duniya.

A daya bangaren kuma, Infantino na ci gaba da yakin neman goyon baya domin sake lashe zaben shugabancin FIFA, inda yake gabatar da kansa a matsayin wanda ke kare muradun kasashe masu karamin karfin tattalin arziki a fagen kwallon kafa.

Infantino ya ce FIFA na da nauyin rage tazarar tattalin arziki tsakanin kasashe mambobin kungiyar 211, tare da tabbatar da cewa kasashe masu tasowa su ma suna samun damar bunkasa kwallon kafa da cin gajiyar kudaden FIFA.

Sai dai matsin lamba na ci gaba da karuwa kan Infantino. UEFA, CONCACAF da wasu bangarorin hukumar kwallon kafa ta Asiya na tattauna yiwuwar daukar matakin rashin amincewa da shugabancinsa, yayin da wasu kasashe suka janye goyon bayansu gare shi.

A nahiyar Afirka kuwa, har yanzu kungiyar CAF na daga cikin manyan kungiyoyin da ke nuna goyon baya ga Infantino. Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Kamaru, Samuel Eto’o, ma ya fito fili ya kare Infantino, yana mai cewa wasu daga cikin sukar da ake yi masa na da alaka da siyasar zaben shugabancin FIFA.

Rahotanni sun kuma ce ana ta tattaunawa kan yiwuwar samun wani dan takara da zai kalubalanci Infantino, yayin da wa’adin gabatar da sunayen ‘yan takara ke gabatowa.

Zaben shugaban FIFA na gaba zai kasance daya daga cikin zabukan da suka fi daukar hankali a tarihin kwallon kafa ta duniya, musamman saboda rarrabuwar kawuna tsakanin Turai da wasu daga cikin sauran nahiyoyi kan yadda ake tafiyar da FIFA da makomar kwallon kafa ta duniya.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: Maulidin 2026: IMC Ta Yi Kira Da Ƙarfafa Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Najeriya
Next Post: Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi

Karin Labarai Masu Alaka

Wikki Tourists FC: Ta Yi Sabbin ‘Yan Wasa Uku Wasanni
Najeriya Ta Kai Wasan Kusa Da Na Karshe A Wasan Dambe Na Matasan Afirka Wasanni
Umar Aliyu, Shugaban Magoya Bayan Wikki Tourist Jagorancin Wikki Tourist FC Na Samun Yabo Wasanni
Manchester United Na Dab Da Kammala Daukar Carlos Baleba Daga Brighton Wasanni
An Kaddamar Da Kwamitin Kwallon Kafa A Tsakanin Masarautun Jihar Gombe Labarai
Senegal Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirka Afcon 2025. Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

https://www.youtube.com/watch?v=sainfSmn-EQ

Sabbin Labarai

  • Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna
  • Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi
  • Ceferin Ya Ce Ba Zai Yi Takarar Shugabancin FIFA Ba
  • Maulidin 2026: IMC Ta Yi Kira Da Ƙarfafa Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Najeriya
  • Alejandro Balde Na Dab Da Komawa Manchester United Daga Barcelona

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamna Inuwa Yahaya Ya Amince Da Gyaran Fadar Sarkin Gombe Afrika
  • UPF Ta Bukaci Haɗin Gwiwa Da NERDC Domin Gina Al’umma Mai Zaman Lafiya Afrika
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Talata 11.18.2025 Rediyo
  • Tinubu Zai Gabatar Da Jawabi ga Shugabannin Duniya A Taron UNGA Afrika
  • Wakilan Rasha Da Ukraine Sun Tattauna A Abu Dhabi Ranar Juma’a Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gombe Ta Ƙarfafa Matasa da Ƙwarewar da Za Ta Kai Su Masana’antar Mai Da Iskar Gas Afrika
  • Lakurawa Sun Kashe A Ƙalla A Mutane 34 A Jihar Kebbi Labarai
  • Gwamnatin Bauchi Ta Amince Domin Inganta Kasuwancin Nama A Jihar Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.