Gyaran Kwallon Najeriya Ya Samu Goyon Bayan FIFA Yayin da Shugaban NSC Shehu Dikko Ya Jagoranci Tawaga Zuwa Zurich
Yunkurin sake fasalin harkokin ƙwallon ƙafa a Najeriya ya samu gagarumar dama bayan wata babbar ganawa tsakanin Hukumar Kula da Wasanni ta Ƙasa (NSC) da hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA, a ranar Talata a hedikwatar FIFA da ke Zurich, Switzerland.
Tawagar Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Shugaban NSC, Mallam Shehu Dikko, ta gana da shugabannin FIFA, ƙarƙashin jagorancin Shugaban hukumar, Gianni Infantino.
Ganawar ta mayar da hankali ne kan batutuwan tsarin hukumomi, shugabanci da bunƙasa ƙwallon ƙafa, da kuma hanyoyin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da FIFA.
Shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya bayyana jin daɗinsa da ganawar, yana mai cewa tattaunawar ta ba su damar daidaita ra’ayoyi kan makomar ƙwallon ƙafa a Najeriya.
Infantino ya ce:
«“Na ji daɗin zama da tawagar daga Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar Kula da Wasanni ta Ƙasa (NSC), Shehu Dikko, a Gidan FIFA da ke Zurich, domin gudanar da muhimman tattaunawa da kuma daidaita hangen nesanmu kan ƙwallon ƙafa a ƙasar.”»
Ya bayyana cewa tattaunawar ba ta tsaya kan gasannin ƙwallon ƙafa kawai ba, sai dai ta shafi samar da ingantattun ginshiƙan hukumomi da tsarin gudanarwa da za su taimaka wajen gina ingantaccen tsarin ƙwallon ƙafa mai ɗorewa.
Ya ce sun tattauna dalla-dalla kan harkokin hukumomi, shugabanci, bunƙasa ƙwallon ƙafa da ayyukan haɗin gwiwar da ake gudanarwa.
Infantino ya kuma jaddada buƙatar samar da ingantattun tsare-tsare da hanyoyin ci gaba domin ƙara bai wa matasa damar shiga harkar ƙwallon ƙafa, tare da duba wuraren da FIFA za ta ƙara taimakawa wajen bunƙasa wasan a Najeriya.
A nasa bangaren, Darakta-Janar na NSC, Hon. Bukola Olopade, wanda shi ma ya halarci taron a Zurich, ya ce ganawar ta nuna yadda hukumar ke son yin aiki tare da hukumomin ƙwallon ƙafa na duniya da sauran masu ruwa da tsaki a Najeriya.
Olopade ya ce wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen tabbatar da cewa gyare-gyaren da ake yi sun dace da ƙa’idojin duniya, tare da la’akari da buƙatun musamman na ci gaban ƙwallon ƙafa a Najeriya.
Ya ce:
«“Ga NSC, ganawar Zurich wani muhimmin mataki ne a cikin ƙoƙarin sake fasalin ƙwallon ƙafa a Najeriya ta hanyar ƙarfafa hukumomi, samar da ingantattun hanyoyin bunƙasa ‘yan wasa, inganta shugabanci da kuma samar da ƙarin damammaki ga matasan Najeriya.”»
Hukumar NSC ta kuma jaddada cewa gyaran da ake yi ba wai don amfanin wasu mutane ba ne, sai dai domin gina tsarin ƙwallon ƙafa mai ƙarfi, gaskiya da ɗorewa, wanda zai iya samar da nasara a filin wasa da wajen filin wasa.
Hukumar ta ce, tare da haɗin gwiwar FIFA da sauran masu ruwa da tsaki, za ta ci gaba da aiki domin samar da cikakken tsarin gyara da zai ƙarfafa ƙwallon ƙafar Najeriya tare da buɗe dimbin damar da wasan ke da shi ga ‘yan wasa, masu gudanarwa, matasa da kuma tattalin arzikin wasanni na Najeriya baki ɗaya.
Tawagar Najeriya
Tawagar Najeriya da Shugaban NSC, Mallam Shehu Dikko, ya jagoranta ta haɗa da Darakta-Janar na NSC, Hon. Bukola Olopade; Mai ba Shugaban CAF shawara na musamman kuma Mataimakin Shugaban Kwamitin Gasannin Ƙungiyoyin Ƙasa na Maza na FIFA, Amaju Pinnick; Mukaddashin Sakataren Janar na NFF, Dr. Emmanuel Ikpeme; da Daraktan Sashen Shari’a na NFF, Okey Obi Esq.
Sauran manyan jami’an da suka halarci ganawar sun haɗa da Mataimakin Shugaban CAF na biyu, Kurt-Okraku, da Daraktan Ƙungiyoyin Ƙasashe na FIFA mai kula da Afirka, Gelson Fernandes.


