Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

NFF Ta Nada Eguavoen Kocin Rikon Kwarya Na Super Falcons
Published: September 8, 2026 at 11:44 PM | By: Bala Hassan

 

Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta naɗa tsohon kocin Super Eagles, Augustine Eguavoen, a matsayin kocin rikon kwarya na ƙungiyar mata ta Najeriya, Super Falcons.

Eguavoen zai jagoranci Super Falcons a wasannin neman gurbin shiga Olympics na 2028, inda Najeriya za ta kara da Comoros a zagaye na biyu na gasar neman gurbin shiga gasar.

Super Falcons za ta kara da Comoros a wasanni biyu da za a buga a Remo Stars Stadium da ke Ikenne-Remo, a ranakun 9 da 13 ga Oktoba 2026.

Eguavoen zai samu taimakon Christopher Danjuma, kocin Nasarawa Amazons, da kuma tsohuwar ‘yar wasan Super Falcons, Yusuf, tare da Olatunji Baruwa, wanda a baya ya taba rike aikin horar da masu tsaron raga na Super Eagles.

Wannan shi ne karo na farko da Eguavoen zai jagoranci wata kungiyar mata a matsayin babban koci.

Naɗin nasa ya biyo bayan sallamar Justine Madugu da tawagarsa ta masu horarwa, bayan Super Falcons ta kasa samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta mata ta 2027—karo na farko da Najeriya ta kasa samun gurbin gasar tun bayan fara gasar a shekarar 1991.

Yanzu Eguavoen na fuskantar babban ƙalubale na dawo da Super Falcons kan turbar nasara, musamman a gasar neman gurbin Olympics na 2028.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: Manchester United Na Cikin Manyan Kungiyoyi 10 Na Champions League
Next Post: Dr. Zainab Gwamna Ta Hada Mata Fiye Da 6,000 Domin Haɗin Kai Da Ci Gaba A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

An Shirya Taron Horas Da Matasa Gabanin Wasan Motsa Jiki 2025 Wasanni
Abun Da Kuke Buƙatar Sani Game Da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka 2025 Wasanni
Dangantaka Tayi Tsamari Tsakanin Salah Da Slot. Wasanni
Hawan Durba A Fadar Sarkin Zazzau Afrika
Al Hilal Ta Cimma Yarjejeniya Da Pedro Wasanni
Kocin Newcastle Matthias Ya Ce Lewis Hall Ba Zai Koma Manchester United Ba Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Yeriman Ingila Ya Gana Da Yeriman Saudiya Mai Jiran Gado Amurka
  • Chelsea Tayi Kaca-Kaca Da Barcelona A Gasar UCL Wasanni
  • Gombe Ta Zo Ta Biyu Wajen Aiwatar Da Shirin L-PRES Afrika
  • Kungiyar Kiristoci Ta Karyata Kubutar Da Mambobin Su A Kaduna Afrika
  • Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ Afrika
  • Miliyan Biyar Ko Rayuwata: Barazanar ’Yan Ta’adda Ta Jefa Wani Mazaunin Dukku Cikin Fargaba Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Zata Farfado Da Cibiyar Koyon Sana’oi Ta Dangote Afrika
  • Amurka Tafara Mayar Da ‘Yan Afghanistan Da Suka Makale A Qatar Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.