Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
  • Hukumomin Kashe Gobara A Gombe Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Hana Gobara A Lokacin Bazara Labarai

PDP Ta Amince Da Hukuncin Kotun Tarayya Na Soke Takarar Pantami
Published: September 24, 2026 at 8:04 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jam’iyyar PDP, ta ce za ta bi hukuncin Kotun Tarayya da ke zamanta a Gombe, wanda ya soke zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar a baya domin fitar da ɗan takararta na gwamnan jihar, tare da umartar ta da ta sake gudanar da sabon zabe.

Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar, Malam Jungudo Haruna Mohammed, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce PDP za ta nazarci hukuncin kotun tare da ɗaukar matakan gaggawa domin tabbatar da cikakken bin umarnin da kotun ta bayar.

Ya ce jam’iyyar na nan daram kan ƙa’idodin dimokuraɗiyyar cikin gida, bin ƙa’ida, adalci da kuma kiyaye kundin tsarin mulkinta, ƙa’idojin zaɓen fidda gwani da kuma dokokin Tarayyar Najeriya.

Jungudo ya ce jam’iyyar za ta fara matakan da suka dace domin gudanar da sabon zaben fidda gwani na takarar gwamnan Gombe, bisa umarnin kotun.

Ya ƙara da cewa za a sanar da ranar gudanar da zaben, jadawalin ayyukan da sauran bayanai ga dukkan masu neman takara, masu ruwa da tsaki, mambobin jam’iyyar da kuma sauran jama’a da zarar an kammala shirye-shiryen.

Jam’iyyar PDP ta kuma yi kira ga mambobinta, magoya bayanta da masu ruwa da tsaki a jihar Gombe da su kasance cikin nutsuwa, su kiyaye doka tare da ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai yayin da jam’iyyar ke ɗaukar matakan aiwatar da hukuncin kotun.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Najeriya Da Amurka Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Bunƙasa Harkar Ma’adinai
Next Post: Sauyin Yanayi: Masana A Kaduna Sunyi Kira Ga Yan Kasuwa Su Mayar Da Shara Zuwa Kudi

Karin Labarai Masu Alaka

Yanbindiga sun Kashe kimanin mutane 30 a yankin kayama ta Jihar kwaran Najeriya Najeriya
Najeriya Tayi Asarar Kusan Naira Triliyan 1 Sakamakon Harajin Trump Amurka
Rasha Takai Hari Ukraine Da Jirgi Marar Matuki Afrika
Jana’izar Jagoran Ƙolin Iran Ta Kawo Tsauraran Matakan Tsaro A Tehran Afrika
Amurka Zata Kamallah Yaki Da Iran A Makonni Biyu Masu Zuwa Amurka
Masu Ruwa Da Tsaki 60 Sun Samu Horon Sasanta Rikici Don Ƙarfafa Zaman Lafiya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
  • Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Jihar Filato Ta Sauke Hakimin Mushere Afrika
  • Sabuwar Dama Ga Masu Zaɓe: INEC Ta Tsawaita CVR Zuwa Ƙarshen Yuli Afrika
  • Kotun Daukaka Kara A Faransa Zata Tabbatar Da Hukuncin ‘Yan Jam’iyyar Ra’ayin Rikau Labarai
  • Allah Ya Yiwa Shahararren Dan Jarida Saleh Shehu Ashaka Rasuwa Labarai
  • Rundunar ’Yan Sandan Bauchi Ta Kama Dattijo Kan Zargin Cin Zarafin Yarinya ’Yar Shekara 8 Afrika
  • Tinubu Ya Aika Manyan Hafsoshin Tsaro Borno Afrika
  • An Katse Intanet Da Wayar Tarho A Kasar Uganda Siyasa
  • Janar Christopher Zai Maye Gurbin Ministan Tsaron Najeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.