Hukumar Ba da Agajin Gaggawa a Najeriya wato (NEMA), tare da haɗin gwiwar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar Kebbi (SEMA), sun raba kayan tallafin abinci ga ’yan gudun hijira a ƙananan hukumomi huɗu na jihar Kebbi.
Ƙananan hukumomin da suka amfana da tallafin sun haɗa da Koko-Besse, Zuru, Yauri da Bagudo.
An gudanar da rabon tallafin ne domin rage wa ’yan gudun hijirar wahalhalun rayuwa, tare da samar musu da muhimman kayan abinci da za su taimaka wajen biyan buƙatunsu na yau da kullum.
Kayan tallafin da aka raba sun haɗa da buhunan shinkafa 900, wake buhu 900 da masara buhu 900, baya ga tumatir.
Mista Tukur Abubakar ne ya miƙa kayan tallafin a madadin Daraktar-Janar ta NEMA, Zubaida Umar. Tare da shi akwai Shugaban Hukumar SEMA ta Jihar Kebbi, Alhaji Kabiru Bako; Sakataren Zartarwa na hukumar, TPL Abubakar Abdullahi Tuleje; da Daraktan Kuɗi da Samar da Kayayyaki, Alhaji Mansur Na’Allah.


