Kwamitocin Kasafin Kuɗi na Majalisar Dokokin Amurka sun jaddada kudirin Amurka na tunkarar take-taken addini a duniya, musamman a Najeriya.
Wannan na zuwa ne bayan ziyarar tawagar ‘yan majalisar da Shugaba Donald Trump ya tura ƙarƙashin jagorancin Riley Moore.
A Najeriya, tawagar ta gana da mai bawa Shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, domin ƙarfafa haɗin gwiwar yaki da ta’addanci da tsaro a yankin.
Moore ya kai ziyara Benue, inda ya gana da shugabannin Katolika da na al’ummar Tiv tare da duba sansanonin ‘yan gudun hijira.
Ya bayyana abin da ya gani a matsayin abin tausayi, inda ya ruwaito tashin hankali da kisan gilla da suka tilasta dubban Kiristoci tserewa daga gidajen su.
Ya ce fiye da Kiristoci 600,000 na rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira a Benue. Moore ya kuma yi zargin “harin kisan kare dangi da Fulani suke yi a jihar.
Tawagar ta yaba wa gwamnatin Najeriya kan ceto daliban makarantar Katolika fiye da 100, tare da cewa ƙawancen tsaro tsakanin Najeriya da Amurka ya fara inganta, amma akwai sauran aikin da za a yi.
Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da dangantaka ke ƙara tsami bayan gwamnatin Trump ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargin suna keta ‘yancin addini, matakin da ya haddasa ce-ce ku-ce a bangaren diplomasiya.
Gwamnatin Tarayya ta ce ba a nuna bambanci ga addini, saboda rashin tsaro yana shafar kowa.


