Ranar Litinin, Amurka ta azawa rudunar sojin Rwanda takunkumi da wasu manyan hafsoshin kasar dangane da irin rawar da suke takawa a yaki da ake yi a gabashin jamhuriyar Demokuradiyyar kwango, kuma ta bukaci su janye daga yankin mai albarkatun ma’adinai ba tare da bata wani lokaci ba.
Rwanda dai ta jima tana musanta zargi daga kwango da MDD da manyan kasashen yammacin duniya suke yi mata cewa ita take daurewa Kungiyar ‘yan tawayen M23 gindi, wacce a bara tayi kukan kura a gabashin jamhuriyar kwangon, inda yanzu take rike da kasa fiye da a ko wani lokaci da ake wannan rikici.
Ma’aikatar kudi ta Amurka ta fada ranar Litinin cewa babu yadda za’a yi ‘yan tawayen M23 su sami nasarar kama kasa mai yawa haka ba tare da taimakon Rwanda ba. A nata bangaren ma’aikatar harkokin wajen Amurka tace, saboda goyon bayan da Rwanda take baiwa ‘yan tawayen M23 sun aikata mummunar barna da keta ‘yancin Bil’adama.
A cikin wata sanarwa da ta aikewa kamfanin dillancin labarai na Reuters, gwamnatin Rwandan tace takunkumin bashi da adalci domin ya auna bangare daya ne a yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla, kuma hakan “bai bayyana hakikanin gaskiyar abunda yake kasa ba, kuma ya dagula ainihin rikici da ake yi a yankin.


