Babban Limamin Makarantar Madarasatul Sheikh Usman Muhammad Mai Mota Gwalli da ke Kaduna, Najeriya, ya karrama Fasto Dr. Yohanna Buru da sarautar “Jagoran Zaman Lafiyar Arewacin Najeriya”, bisa la’akari da shekaru 25 da ya shafe yana ƙoƙarin samar da zaman lafiya, juriya a addinai da zaman tare tsakanin al’ummomin addinai daban-daban a Arewacin Najeriya.
Sheikh Usman Muhammad Mai Mota Gwalli ne ya jagoranci tawagar fitattun malaman addinin Musulunci zuwa cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry da ke Bagyi Villa, a Kaduna, domin karrama faston bisa gudunmawar da ya bayar tsawon shekaru wajen ƙarfafa alaƙar addinai da inganta fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kiristoci.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Sheikh Usman ya bayyana cewa sun zo ne domin nuna godiya da kuma karrama Fasto Buru bisa jajircewarsa wajen inganta haƙuri, yafiya, ƙauna, haɗin kai da kyautatawa tsakanin mutane ba tare da la’akari da ƙabila, al’ada ko yankin da suka fito ba.
Ya ce: “Mun zo ne domin gode maka bisa sadaukarwarka da cikakken ƙoƙarinka wajen inganta zaman lafiya, yafiya, ƙauna, haɗin kai da kyautatawa ga dukkan bil’adama, ba tare da la’akari da ƙabila, al’ada ko yankin da mutum ya fito ba.
“Mun zo a matsayin tawagar malaman Musulunci domin karrama Fasto Dr. Yohanna Buru tare da gode masa bisa ƙoƙarinsa na dawo da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin ’yan Najeriya.”


