Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

An Gudanar Da Taron Matasan Kasashe 6, Don Kawo Karshen Ta’addanci
Published: November 20, 2025 at 3:09 PM | By: Yusuf Aliyu Harande

An gudanar da wani taron wayar da kan matasa daga kasashe 6 na yankin sahel a Jamhuriyar Nijar. Taron na wuni biyu da zummar tattauna hanyoyin kare matasa daga masu aikata aiyukan asha.  A karshen wannan zama mahalartan za su fitar da wani kundin da za a gabatar wa hukumomi domin daukan matakai.

La’akari da irin barazanar da matasa ke fuskanta daga masu tafka ta’asa a fannoni irin su tsaro ko siyasa, Tattalin arziki da sauransu ya sa kungiyar kasa da kasa ta Gorée Institute shirya wannan taro na wuni 2 domin matasan yankin sahel, a wani yunkurin bai wa wannan rukuni dama wajen tafiyar da lamura a gwamnatance.

Ministan matasa da wasannin motsa jiki na Nijar Mohamed Sidi shi ne ya jagoranci bikin bude wannan zama. Ya kuma bayyana fata game da yadda ya kamata matasa su kasance a nan gaba.

A yayin mahwarorin da za su yi a wannan haduwa mahalartan zasu tsaida shawarwari na bai daya, wadanda su ke kallo a matsayin mafitar matsalolin da ke jefa matasa bin hanyoyin da ba su dace ba, kamar yadda Awal Oumarou Ibrahim ya bayyana.

Taron Wanda shine karo na 6 da ake shirya makamancinsa na samun halartar jagororin matasa daga kasashen Senegal, Mali, Cote D’ivoire, Burkina Faso, Jamhuriyar Benin da Nijar mai masaukin baki.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: Rasha Na Cigaba Da Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Ga Ukrain
Next Post: Kungiyar Enyimba: Bamu Da Niyyar Rage Albashin ‘Yan-Wasa

Karin Labarai Masu Alaka

An Dakatar Da Daniel Bisa Zargin Fyade Wasanni
Arteta, Arsenal Zata Yi Sauye-Sauye A Janairu, Wasanni
Manya-Manyan Wasannin Wannan Makon Wasanni
FIFA, Ta Tabbatar Da Ranar Mika Sunayen ‘Yan Wasa AFCON 2025. Wasanni
An Bude Gasar Kwallon Kafa Ta Mata A Najeriya NWFL 2025 Wasanni
Wikki Tourist FC: Ta Sallami ‘Yan Wasa Hudu Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Jam’iyar APC A Najeriya Ta Kaddamar Da Bada Shaidar Zama Dan Jam’iyyar Ta Na’ura Mai Kwakwalwa
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Mawakiyar Amurka Cardi B. Ta Cashe A Saudi Araibiya Nishadi
  • Gwamnatin Najeriya Ta Horar Da Matasa Sama 7,000 A Matsayin Masu Tsaron Daji Labarai
  • ‘Yan-Ta’adda Sun Yi Ma Wasu Mutane Yankan Rago A Jihar Neja Labarai
  • Akwai Bukatar Bincikar Umurnin Da Sakataren Tsaro Pete Ya Bada Amurka
  • Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Christ Musa Ministan Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Fiye Da Fararen Hula 1000 Yunwa Ta Kashe A Sudan Afrika
  • Shugaba Trump Ya Hana Kaiwa Cuba Man Fetur Daga Venezuela Amurka
  • Ministocin Kasar Asia Zasu Gudanar Da Taro A Kasar Malaysia Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.