Kasar Senegal ta kara wa’adin zaman kurkuku daga shekaru 5 zuwa 10 ga duk wanda aka kama yana mu’amala da jinsi daya, kuma ta haramta duk wata harka ta luwadi. Dokar ta samu goyon bayan ‘yan majalisa su 135.
Wannan doka na daya daga cikin alkawuran da gwamnati mai ci ta shugaban kasa Bassirou Diomaye Faye da kuma prime minista Ousmane Sonko tayi lokacin yakin neman zabe. Yanzu dokar na jiran sa hannun shugaban kasa Diomaye Faye.
Dama tun da dokar hukunta Senegal, Wadda aka yiwa gyare-gyare a shekarar 1966 ta tanadi daurin shekaru 5, da kuma tara har zuwa kimanin miliyan daya da dubu dari biyar na kudin kasar, wanda yayi daidai da dala 2,700, ga duk wani da aka kama ga aikata laifin aure ko mu’amula ta jinsi daya.


