Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ADC Ta Kaucewa INEC Ta Gudanar Da Babban Taro Labarai
  • Za A Cigaba Da Tattaunawa Domin Kawo Karshen Yakin Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

An Sako Ɗaliban Makaranta 130 Da Aka Sace A Jihar Neja 
Published: December 21, 2025 at 8:30 PM | By: Bala Hassan

An sako Ɗaliban makaranta 130 da aka sace a Jihar Neja

An saki dukkan ɗaliban makaranta da aka sace daga makarantar St. Mary’s Catholic School da ke Papiri a Jihar Neja.

An kubutar da rukunin ƙarshe mai ɗalibai 130, lamarin da ya kai adadin waɗanda aka ceto gaba ɗaya zuwa 230.

Jami’an Ofishin Mai baiwa sugaban kasa shawara kan harkokin tsaron Ƙasa sun tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Lahadi.

Wannan cigaba ya kawo ƙarshen kwanaki na damuwa da tashin hankali da iyalan waɗanda abin ya shafa suka shiga, da kuma nuni da gagarumar nasara ga hukumomin tsaro,da suka jagoranci aikin ceton.

An sace ɗaliban ne lokacin da ’yan bindiga suka kai hari makarantar kwanan, lamarin da ya haifar da ƙorafi a faɗin ƙasar tare da sake tayar da muhawara kan batun tsaron makarantu a Najeriya.

Hukumomi sun bayyana cewa sakin dukkan waɗanda aka sace ya biyo bayan matsin lambar jami’an tsaro ba kakkautawa da kuma haɗin gwiwa tsakanin hukumomi, yayin da ake ƙara kira ga ƙarfafa tsaron makarantu da ɗaukar matakan da suka dace domin hana faruwar irin waɗannan hare-hare nan gaba.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: An Dakatar Da Daniel Bisa Zargin Fyade
Next Post: Yau Litinin Za’a Mika Daliban Ga Iyayen Su

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Ta Yi Juyin Mulki A Kasar Venezuela Amurka
Allah Ya Yi Wa Sheikh Dahiru Bauchi Rasuwa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Thailand Da Cambodia Sun Fara Tattauunawa Kan Batun Tsagaita Wuta Labarai
Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Guinea Bissau Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
‘Yansandan Uganda Sun Tsare ‘Yar Fafutukar Kare Hakkin Bil’adama Sarah Bireete Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Matatar Man Dangote Zata Wadatar Da Najeriya Da Makota Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Gwamnatin Najeriya Zata Rabawa Al’umma Tallafin Noma
  • Shugaba Trump Ya Yabawa Iran Bisa Bude Mashigar Hormuz
  • Shugaba Tinubu Yasa Hannu Kan Dokar Kasafin 2026
  • Shugaba Tinubu Yace Bazai Bawa ‘Yan Najeriya Kunya Ba
  • Jami’an Askarawa A Zamfara Sun Kama Na’urorin Fashewa Da Makudan Kuɗaɗe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rundunan  ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Ta Miƙa Miyagun Ƙwayoyi Da Ta Kama Wa NDLEA. Labarai
  • Kasar China Ta Kaddamar Da Rawar Daji A Yankin Taiwan Labarai
  • Kungiyar Kiristoci Ta Wanke Gwamnan Bauchi Daga Zargin Ta’addanci Labarai
  • Kungiyar Kwadago Ta NLC Ta Gudanar Da Zanga-Zanga Bisa Matsalar Tsaro Tsaro
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane A Hare Hare Daban Daban A Najeriya Najeriya
  • CAF Ta Dakatar Da Kocin Senegal Pape Thiaw Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Hadakar Gwamnatin Najeriya Da Amurka Ne Suka Kai Hari Sokoto Najeriya
  • Zanga-Zangar Adawa Da Harin Amurka Da Isra’ila Ya Zamo Tarzoma A Pakistani Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.