An ji karar wasu fashe fashe a birnin Maiduguri a daren jiya Litinin sakamakon wani hari da aka a birnin, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da jikkata wadansu, kamar yadda gwamnatin jihar da mazauna birnin suka fada.
Wasu feya-feyan video da suke yawo a dandalin sada zumunta sun nuna masu aikin agaji a wani asibiti dake birnin na Maiduguri suna taimakon wadanda suka ji rauni da sutura jina-jina, kmfanin dillancin labarai na Reuters ba zai shaida sahihancin wadan nan videoyin ba.

Gwamnan jahar Babagana Zuluma cikin sanarwa da ya bayar, yace harin ya halaka mutane da jikkata wasu, sai dai bai bada karin bayani kan ko wa yake da alhakin kai harin ba.
Muna da karin bayani bayan labaran duniya a Rahoton da Wakilin GTA Hausa Amurka Ke Magana ya aiko mana


