Shugaban ƙasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya bayar da kyaututtuka sama da dala 130,000 da kuma filayen bakin teku ga kowanne memba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar bayan nasarar da suka samu a wasan ƙarshe na gasar cin kofin ƙasashen Afirka da suka fafata da Morocco ranar Lahadi.
Faye ya yi jawabin ne a wani biki da aka yi a babban birnin Dakar a daren Talata inda dubban magoya bayan ƙungiyar suka fito kan tituna don tarbar ƙungiyar Lions of Teranga da ta yi nasara.
Senegal ta doke Morocco mai masaukin baki da ci 1-0 bayan ƙarin lokaci, dan wasan ta Pape Gueye ya jefa kwallon a mintuna huɗu bayan ƙarin lokaci (extra time).

A safiyar Talata, ‘yan wasan Senegal sun hau wata mota kirar bas da aka lulluɓe da kalmomin “zakarar Afirka” a titin Dakar zuwa fadar shugaban ƙasa.
Karin kuɗin CFA miliyan 75 ($134,892.09) ga kowanne daga cikin ‘yan wasa 28 na ƙungiyar, jimillar kuɗin CFA biliyan 2.1 ko dala miliyan 3.7.
Bayan haka ‘yan wasan za su samu kyautar filaye mai fadin murabba’in mita 1,500 ko wannen su.
Bayan haka, Faye ya ce membobin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Senegal za su sami kuɗi CFA miliyan 50 da fili mai fadin murabba’in mita 1,000, yayin da membobin tawagar Senegal da suka je Morocco za su sami kuɗi CFA miliyan 20 da fili mai fadin murabba’in mita 500.
Ya ce ma’aikatan wasanni suma za su sami garabasar kuɗi CFA miliyan 305 a matsayin kari.


