Burkina Faso ta saki mayakan Najeriya su 11 wadanda ta tsare fiye da mako guda da ya shige, a bayan da jirginsu yayi saukar gaggawa.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya fada ranar alhamis cikin wata sanarwa ta kafar X cewa an warware batun matuka jirgin saman yakin Najeriya da mutanen dake cikin jirgin ta hanyar diflomasiyya.
Sanarwar ta ce gwamnatin mulkin soja ta Burkina Faso a karkashin jagorancin Ibrahim Traore, ta sako sojojin saman a bayan ganawa da wata tawagar Najeriya karkashin jagorancin Tuggar.
A makon da ya shige rundunar mayakan saman Najeriya ta ce jirgin yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Portugal domin sabis da aka saba yi ma jirage a lokacin da yayi saukar gaggawa a garin Bobo Dioulasso a yammacin Burkina.
Amma kuma gidan talabijin na kasar Burkina Faso ya watsa wani jawabin ministan harkokin wajen Najeriya Tuggar ranar laraba, inda yake cewa an bi ta hanyoyin da ba su dace ba wajen neman izinin wucewar jirgin ta samaniyar kasar, ya kuma nemi ahuwar hakan.
Shugaban gwamnatin mulkin soja ta kasar Mali, Janar Assimi Goita, ya ce saukar gaggawar da jirgin na Najeriya yayi, ya sa Kungiyar Kasashen Yankin Sahel ta sanya dakarun tsaron samaniyarta cikin shirin ko ta kwana, tare da ba su iznin harbo duk wani jirgin da ya shiga samaniyar yankin ba tare da izni ba.
Wannan kungiya ta kunshi kasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar.
Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce a yanzu matuka jirgin saman zasu wuce da shi wurin gyara a kasar Portugal.


