Kocin Najeriya Éric Chelle ya ce rashin jituwa tsakanin Victor Osimhen da Ademola Lookman a filin wasa zai zama matsala ta cikin gida bayan da Super Eagles ta samu shiga zagayen kungiyoyi 8, a gasar cin kofin AFCON ta 2025.
Lamarin ya faru ne a rabin lokaci na biyu lokacin da Osimhen da Lookman suka shiga wata takaddama a filin wasa bayan wani harin da su kai.
Kyaftin Wilfred Ndidi ya shiga tsakani nan take, inda ya raba ‘yan wasan biyu ya kuma dawo da kwanciyar hankali kafin a ci gaba da wasan.

Da yake magance lamarin bayan wasan, Chelle ya ki bayar da cikakkun bayanai, yana mai dagewa cewa ba za a tattauna shi a bainar jama’a ba.
“Ba na bukatar in gaya muku abin da zai faru, ina ajiye dashi a kaina.”in ji Chelle.


