Bayan shafe makonni bakwai suna hutun dole, daliban makarantun firamare da sakandare a jahar filato sun koma azuzuwa don ci gaba da neman ilimi.
Rufe makarantun da gwamnatin jahar Filato ta yi a watan Nuwamban bara, ta ce ta yi ne don yin rigakafi, sakamakon matsalolin tsaro da garkuwa da dalibai da ‘yan bindiga suka yi a wassu jihohin Najeriya,
Wassu daliban firamare na makarantar gwamnati ta Obasanjo Model School dake Jos, Favour Francis Daniel da Yane Iliya Bulus Choji sun bayyana yadda zasu tinkari jarabawa bayan dawowarsu daga hutun dole.
Shugaban sashen makarantar Obasanjo Model School Jos, Mangai Obi Maren yace yayi farinciki da daliban suka dawo a ranar farko.
Da shike tun farko gwamnati ta rufe makarantun ne saboda tsaro, na garzaya ofishin shirin samadda tsaro a makarantun jahar Filato.
Daraktan tsare-tsare na shirin, Mr Ben Chikan yace gwamnati ta hada kai da masu ruwa da tsaki don samadda tsaro a makarantun jahar.
Sakatare a hukumar ilimin bai daya matakin farko a jahar Filato, Tang’an Emmanuel yace ya zaga makarantun ya kuma ga yadda malamai da dalibai suka dukufa wajen koyo da koyarwa.
Jihohi tara ne a fadin Najeriya suka rufe makarantu a watan Nuwamban dubu biyu da ishirin da biyar, yayinda gwamnatin tarayya ta rufe makarantun unity arba’in da bakwai a fadin kasar, wanda a yanzu kudan dukkan jihohin sun umurci dalibai su koma makarantu, in banda jahar Edo da ita ma ta umurci makarantun su kasance a rufe saboda matsalolin tsaro.


