Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Farashin Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya
Published: March 28, 2026 at 8:30 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Farashin mai a kasuwanni duniya ya tashi ranar jumma’a, saboda shakkun da ake dashi na yi yuwar a tsagaita wuta a yakin nan da yanzu aka yi wata guda ana gwabzawa, duk da haka wannan ne makon farko da mai mafi daraja da ake kira Brent farashinsa zai sassauto, bayanda shugaban Amurka Donald Trump yace shawarwari da Iran suna tafiya yadda ya kamata, ba tare da ya bada wani karin bayani ba.

Farashin mai na Brent ya haura da dala 3 da centi 51, ya tsaya kan dala 111 da centi 52 kan ko wace ganga, yayinda mai da ake kira West Texas ya tashi da dala 4 da centi shida, ya tsaya kan dala 98 da centi 54 akan ko wace gangar danyen mai.

Farashin man mai da daraja da ake kira Brent ya karu da kashi 53 cikin dari tun ranar 27 ga watan Febwairu, kwana daya kamin Amurka da Isra’ila su kaddamar da yakin kan Iran, amma ya ragu da kasa da kashi daya makon nan, shi mai da ake kira West Texas, ya karu da kashi 45 cikin dari tun fara yakin, kuma kullum sai karuwa yake yi sannu a hankali.

‘Yan kasuwa suna taka tsantsan kan kalaman shugaba Trump game da shawarwari da Iran.

Wani jami’in Iran ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, sharuddan da Amurka ta gabatar mata ta hanun Pakistan babu adalci a ciki.

Labarai, Sana'o'i, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Kasashen Yankin Gulf Sun Bada Sanarwa
Next Post: Hamas Ta Kwance Damara

Karin Labarai Masu Alaka

Iran Ta Bukaci Duniya Ta Shirya Domin Fuskantar Tsadan Mai Amurka
Anfara Samun Sakamakon Wucin Gadi a Kasar Guinea Conakry Labarai
Kamfanin Hakar Ma’adanai Na Kasar Kanada Ya Cigaban Da Aikinsa Labarai
Rundunar Sojin Amurka Sunfara Ficewa Daga Kasar Sham Amurka
Gabannin Harin Amurka Da Isra’ila Iran Farisa Ta Shirya Nata Afrika
Anyi Sallar Rokon Ruwa A Saudiya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Belarus Zata Taffawa Jamhuriyar Nijar Afrika
  • CAN: Da Alamu Daliban St. Mery Na Cikin Koshin Lafiya Najeriya
  • An Bude Gasar Kwallon Kafa Ta Mata A Najeriya NWFL 2025 Wasanni
  • Tinubu Ya Aika Manyan Hafsoshin Tsaro Borno Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Zata Farfado Da Cibiyar Koyon Sana’oi Ta Dangote Afrika
  • Kasar Israela Zata Gina Sansani A Gaza Afrika
  • An Kafa Majalisar Kotun Sulhu Ta Kano Labarai
  • Boko Haram Ta Kai Hari Maiduguri Cikin Dare Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.