Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gobara Mafi Muni Cikin Shekaru 60 A Hong Kong Ta Hallaka Rayuka
Published: November 27, 2025 at 7:12 PM | By: Nafisa Ahmad

Wutar gobara mafi muni da aka gani a Hong Kong cikin shekaru fiye da 60, ta kwana tana ci, inda ya zuwa yanzu an ce akalla mutane arbain da hudu (44) ne suka mutu, yayin da ba a san inda wasu dari biyu da saba’in da tara (279) suke ba.

Har yanzu dai jami’an agaji suna ci gaba da zakulo mutane daga benayen da har zuwa safiyar nan suna ci da wuta.

‘Yan sanda sun kama mutane uku bisa zargin haddasa mutuwa dangane da wannan wuta da ta fara tashi tun jiya laraba da tsakar rana. Ya zuwa safiyar yau Alhamis agogon Hong Kong, ba a iya kashe wutar baki daya ba.

Jami’ai sun ce arba’in (40) daga cikin mutanen sun mutu a wurin ne, sauran hudu (4) kuma a asibiti. Wasu mutanen su akalla sittin da biyu (62) sun samu raunuka, wasu kunar wuta, wasu kuma shakar hayaki.

Mutanen da aka kama suna da alaka da kamfanin kwangila da ya gina benayen, inda ake tsammanin an yi amfani da wasu kayayyakin da ba su iya jure ma wuta, abinda ya saba doka.

Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Allah Ya Yi Wa Sheikh Dahiru Bauchi Rasuwa
Next Post: Wani Dan Bindiga Ya Harbi Dakarun Tsaron Cikin Gida Su Biyu A Washington DC

Karin Labarai Masu Alaka

Rasha: Zamu Ba Gwamnatin Venezuel Gudunmawa Sauran Duniya
Asusun IMF Zai Bawa Kasar Misra Lamunin Sama Da Dala Biliyan 2 Sauran Duniya
Ana Jimamin Mutuwar Giwa Mai Shekaru Kusan 60 A Kasar Kenya Sauran Duniya
Netanyahu: Zamu Kashe Dala Billiyan $110 Cikin Shekaru Hudu Don Kera Makamai Sauran Duniya
Somaliya: Ba Za Mu Dauki Wulakancin Donald Trump Ba! Sauran Duniya
Ukraine Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Tsarin Cimma Yarjejeniya Sauran Duniya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Sanatan Nasarawa Ta Arewa Ya Rasu A Kasar India Najeriya
  • An Hana Yada Rahotannin Siyasa A Kasar Uganda Tsaro
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Alhamis 11.20.2025 Rediyo
  • Isra’ila Ta Dau Alwashin Kawo Karshen Falasdi Labarai
  • Gwamna Zulum: Ya Bukaci Sojoji Su Cigaba Da Yakar Boko Haram Da ISWAP Labarai
  • Nnamdi Kanu Ya Nemi A Mayar Da Shi Abuja Daga Gidan Yarin Sokoto Labarai
  • Kasar Iceland Ta Kauracewa Bikin Gasar Wakokin Shekara Mai Zuwa Labarai
  • An Saka Dokar Hana Fita A Karamar Hukumar Lamurde Jihar Adamawa Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.