Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gobara Ta Tashi A Makarantar Koyon Jinyar Dabbobi Dake Jihar Kano
Published: January 22, 2026 at 5:51 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wata gobara da ta tashi a ranar Litinin ta ƙone ajujuwan karatu 34 a wata makarantar kiwon lafiyar dabbobi da ke karamar hukumar Kabo a jihar Kano.

A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara ta ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:53 na rana.

Sanarwar ta ce dakin kula da gobara na hukumar ya karɓi kiran taimako daga wani Jamilu Abubakar, wanda ya ba da rahoton tashin gobara a cikin makarantar. Nan da nan aka tura ma’aikatan kashe gobara daga tashar Rijiyar Zaki zuwa wurin da lamarin ya faru.

“Da suka iso wurin, ma’aikatanmu sun gano wani ginin bene na ƙasa mai fadin ƙafa 500 da tsayin ƙafa 500, da ake amfani da shi a matsayin wajen kiwon lafiyar dabbobi, yana ƙonewa cikin wuta,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa dakuna 16 sun lalace sosai, yayin da wasu 18 suka samu lalacewar ɓangare-ɓangare saboda gobarar.

Sai dai an samu nasarar dakile wutar, inda aka hana ta yaɗuwa zuwa sauran dakuna da ofisoshi a cikin cibiyar.

“An tura motar kashe gobara guda ɗaya daga tashar Rijiyar Zaki don dakile lamarin, in ji sanarwar, wadda ta danganta nasarar aikin da saurin martanin ma’aikatan kashe gobara.

Ba a samu rahoton mutuwar kowa ba a lokacin da ake rubuta wannan rahoto, yayin da ba a bayyana musabbabin gobarar ba.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Shugaba Trump Ya Janye Karbar Kudin Fito Daga Wasu Kasashen Turai
Next Post: Bassirou: Tawagar Senegal Zasu Samu Kyautar Kudi Da Filaye Sakamakon Nasarar Da sukayi AFCON 2025

Karin Labarai Masu Alaka

Fubara Yana Yiwa Dimokraɗiyya Zagon Kasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Dangote Ya Bukaci ICPC Ta Binciki Shugaban NMDPRA Najeriya
Babangida: Hakika Abiola Ya Lashe Zaben Watan Yuni 1993 Labarai
Mizanin Tattalin Arzikin Najeriya Na 2024 Ya Karu Da Kashi 3.84% Labarai
Matsalolin Masarautun Kano Sun Kawo Karshe Najeriya
Wata Tankar Mai Ta Kife A Apapa Legas Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Muna Kokarin Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Gombe – Uwargidan Gwamna
  • Majalisar Dattawar Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet
  • Yeriman Ingila Ya Gana Da Yeriman Saudiya Mai Jiran Gado
  • Dubban Mutane Sunyi Zanga-Zanga A Kasar Australia
  • Bangladesh Tasamu Rangwamen Harajin Da Amurka Ta Kakaba Mata

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • ‘Yan Wasan Kwallon Kafar Najeriya A Shirye Suke Wasanni
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Tabbas Za’a Gudanar Da Gasar Firimiya Lig Ta Najeriya Wasanni
  • An Shirya Taron Horas Da Matasa Gabanin Wasan Motsa Jiki 2025 Wasanni
  • Ukraine Ta Mika Wa Amurka Daftarin Yarjejeniya Da Rasha Sauran Duniya
  • Hamas Ta Mika Ma Isra’ila Gawar Daya Daga Cikin Mutane Biyu Sauran Duniya
  • Sabunta Manhajar Ilimi A Duk Matakai Nasara Ce! Najeriya
  • Dusar Kankara Ta Hana Jirage Tashi A Birnin Paris Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.