Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamna Abba Ya Gana Da Kwankwaso Kamun Ganawarsa Da Tinubu
Published: January 11, 2026 at 1:50 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 11, 2026

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gudanar da wata ganawar sirri da jagoran jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, a gidansa da ke Miller Road, Kano, gabanin tafiyarsa zuwa ƙasar Faransa domin ganawa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Rahotanni sun nuna cewa ganawar ta gudana ne a daren Talata, 6 ga Janairu, 2026. Majiyoyi sun bayyana cewa gwamnan ya isa gidan Kwankwaso da tsakar dare, cikin wata mota mai duhu.

Majiyoyi sun ce tattaunawar ta ɗauki sama da awa guda, amma bayanai sun nuna cewa gwamnan bai samu nasarar shawo kan Sanata Kwankwaso ba domin ya bi shi zuwa jam’iyyar APC, kamar yadda ake zargin akwai matsin lamba daga wasu manyan mutane.

Bayan kammala ganawar, washe gari, Sanata Kwankwaso ya yi jawabi ga magoya bayansa a gidansa, inda ya jaddada cewa ba shi da “farashi” a siyasa kuma yace cin amana ba abu ne mai kyau ba, yana mai nuni da matsalolin tsaro da tattalin arziki da ke rage farin jinin jam’iyyar APC a idon jama’a.

“Wasu na cewa a Nijeriya kowa na da farashi. Idan kana neman wanda ba shi da farashi, ka zo wurin Rabiu Kwankwaso,” in ji shi.

Rahoton ya ce shirin gwamnan na sauya sheƙa zuwa APC ya fuskanci cikas bayan shugabannin jam’iyyar sun lura da martanin jama’ar Kano, Duk da cewa wasu ‘yan majalisar dokoki na NNPP a matakin jiha da ƙasa, da kuma wasu shugabannin ƙananan hukumomi, na shirin sauya sheƙa tare da gwamnan, mafi yawan magoya bayan NNPP a jihar sun ci gaba da nuna cikakken goyon baya ga Kwankwaso.

Wata majiya ta bayyana cewa shugabannin APC na sa ido sosai kan halin da ake ciki a Kano, inda magoya bayan Kwankwasiyya ke nuna karara cewa suna tare da Kwankwaso.

Majiyar ta ce idan gwamnan ya shiga APC, akwai yiwuwar ɗan takarar da Kwankwaso ya goyi baya ya samu ƙuri’u masu yawa sakamakon ramuwar gayya.

Majiyoyi sun kuma ce Shugaban kasa na ci gaba da yunƙurin ganin Kwankwaso ya shiga APC, abin da ya sa ake neman shawo kansa ta hanyoyi daban-daban.

Rahoton ya ƙara da cewa ana sa ran gwamnan zai gabatar wa Shugaban kasa cikakken bayani kan sakamakon ganawarsa da Kwankwaso, tare da tsara matakan tafiyar da al’amuran jam’iyya idan ya yanke shawarar sauya sheƙa.

A halin yanzu, manyan shugabannin APC a Kano, ciki har da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje, mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin, shugaban jam’iyyar APC na jiha Abdullahi Abbas, da Nasiru Gawuna da Murtala Garo, sun dawo ƙasar nan bayan hutun ƙarshen shekara da aikin Umrah.

Ana sa ran Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sanar da matsayinsa kan batun sauya sheƙa ne bayan kammala shawarwari da shugabannin APC a jihar.

Siyasa

Post navigation

Previous Post: Wikki Tourist FC: Ta Sallami ‘Yan Wasa Hudu
Next Post: Habasha Tafara Gina Filin Jirgin Sama Mafi Girma A Afirka

Karin Labarai Masu Alaka

Kauran Gwandu Zai Inganta Wutan Lantarki A Kebbi Siyasa
Gwamna Kefas Na Jihar Taraba Ya Karbi Shaidar Jam’iyar APC Siyasa
Samar Da Tsaro A Jihar Kano Ba Sai An Sa Siyasa Ba! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Katse Intanet Da Wayar Tarho A Kasar Uganda Siyasa
Gwamna Fubara: Rashin Kariya daga PDP Ne Ya Tilasta Ni Komawa APC Siyasa
Wike: Bazamuyi Sake Fubara Ya Sake Samun Nasara Ba Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Babban Hafsan Sojan Libya Ya Mutu A Wani Hatsarin Jirgin Saman Turkiyya Afrika
  • Layin Raba Wutan Lantarki Na Najeriya Ya Fashe Labarai
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Majalisar Tarayya Ta Amince Da Mutane Uku A Matsayin Jakadun Kasashen Waje Labarai
  • Gangamin Wayar Da Kai Don Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Jihar Gombe Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kananan Hukumomi Na Kokarin Karbar Kudadensu Daga Jihohi Najeriya
  • Ukraine Ta Mika Wa Amurka Daftarin Yarjejeniya Da Rasha Sauran Duniya
  • An Bude Makarantu A Najeriya Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.