Gwamnatin jihar Bauchi ta amince da fitar da naira miliyan 97 domin sabunta masana’antar sarrafa nama ta jihar da ke Bauchi, a wani bangare na kokarinta na farfado da harkokin kiwo da sarrafa nama a jihar.
Kwamishinan Ma’aikatar kyautata Kiwo, Dr. Musa Lukshi ne ya bayyana hakan yayin wani ziyarar duba ci gaban aikin da ake yi a masana’antar.
Ya ce kudaden da Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad ya fitar da gaggawa, alama ce ta kudurin gwamnati na inganta darajar sarkar kiwo da kara tabbatar da inganta abinci da ake samarwa al’umma.
Dr. Lukshi ya ce aikin sabuntawar zai hada da girka kayan aiki na zamani, wanda zai taimaka wajen ingantawa tare da tsaftace tsarin aiki da kuma ingancin nama da ake samarwa.
Ya kara da cewa bayan kammala aikin, masana’antar za ta samar da guraben ayyukan yi ga matasa da sauran ma’aikata, tare da bunkasa tattalin arziki da kudaden shiga ga jihar.
Masu kiwo da sauran masu ruwa da tsaki sun bayyana jin dadinsu da shirin, suna masu fatan zai samar da kasuwa mai dorewa, inganta farashi, da rage asarar da ake fuskanta bayan yanka.


