A kalla mutane 70 ne suka rasa rayukan su, yayin da 30 suka jikkata a wani hari da aka kai kusa da Petite Riviere a kasar Haiti, a cewar wata kungiyar rajin kare hakkin dan Adam ranar Litinin. Wannan adadi ya zarta adadi na mutane 16 da hukumomi suka ce an kashe.
Jami’ai da mazauna wajen sun shaidawa kafar yada labarai a garin cewa, harin ya fara ne da duku-dukun safiyar Lahadi a kauyukan dake kusa da birnin Jean denis, ya ci gaba har zuwa safiyar Litinin, inda ‘yan daba suka bazama wajen suna cinnawa gidaje wuta.
Kungiyar rajin kare hakkin dan adam a kasar tace tayi kiyasin mutane 6000 sun rasa matsuguninsu saboda rikicin. Majalisar Dinkin Duniya kuma tayi kiyasin fiye da mutane 2000 sun kaura daga gidajen su kwanaki da suka wuce bayan wasu ‘yan ta’adda sun kawo hari kusa da wajen.


