Wasu jami’an tsaron Najeriya sun bada tabbaci ga ‘yan kasar cewa babu wani abun tashin hankali ko fargaba gameda jiragen leken asiri na Amurka da suke shawagi a sararrin samaniyar kasar. Suka ce matakin ya faranta musu rai saboda Amurka tana taimakawa Najeriya ne ta fuskar tsaro.
Jami’an tsaron sun tabbatarwa Amurka Ke Magana cewa matakin na hadin gwiwa ne tsaknin jami’an tsaron Amurka da mayakan sama na Najeriya. Suka ce akwai sojojin sama na Najeriya a cikin jiragen da suke aikin leken asirin a sararin samaniyar kasar.
Jiragen suna tashi ne daga Ghana. Wannan matakin ya biyo bayan shawarwari da jami’an gwamnatin Najeriya suka yi da gwamnatin Amurka, bayan da shugaban Amurka Donald Trump, yayi barazanar kai hari kan Najeriya domin kare kiristocin kasar wadanda ake zargin ana yi musu kisn kare dangi. Gwamnatin Trump ta amince zata taimaki Najeriya ne bayan da aka gabatar mata da irin kalubale da kasar take fuskanta ta fuskar tsaro.
Gameda zargin gwamnatin Najeriya tana biyan kudin fansa kamin a saki mutane da ake garkuwa da su, musamman dalibai daga makarantu da ‘yan bindiga suke sace su, jami’an tsaron sun rantse da Allah cewa babu sisin kwabo daga aljihun Najeriya da yake fita domin biyan kudin fansa.
Daga nan suka yi kira ga ‘yan Najeriya su daina yi wa matakan gwamnati bahaguwar fahimta, maimakon haka a kullum su bukaci bayani, kamin su yanke shawara kan batu da ya shafi gwamnati da al’uma.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya buga labarin zirga-zirgar jiragen leken asirin sararin samaniyar Najeriya.


