Jam’iyar APC mai mulki a Najeriya ta fara aikin bada katin zama dan jam’iyyar ta na’ura mai kwakwalwa da ake kira e registration a fadin kasar,
Wannan dai shine karon farko da wata jam’iyyar siyasa tabi irin wannan tsari wajan bada katin zama dan jam’iyya a kasar,
Tini dai masu ruwa da tsaki a jam’iyyar suka dukufa wajan fadakar da masu shiga fatin akan muhimmancin karbar katin ta wannan tsari,
Alh Mu’azu Bawa Rijau shine Shugaban APC a Yankin jihohin Arewa Maso tsakiyar Najeriya Wato North Central yace samun ci gaba ne yasa suka dauko tsarin na e registration…
Masana harkokin mulki da kundin tsarin mulki a Najeriyar sunce tsarin na e registration bai sabawa dokar kasarba,
Barista Muhammad Tanko Zakari tsohon mataimakin Ma’ajin kudi ne na APC a Najeriya yace yace da shakku akan duk wani mai kalubalantar APC akan wannan mataki..
A halinda ake dai jam’iyyar APC na Shirin gudanar da zabubbukan Shugabanin ta a matakan jihohi da kananan Hukumomi da Kuma gundumomi a fadin Kasar.
Ga Cikekken Rahoton Mustapha Nasiru Batsari Daga Minna jihar Neja Najeriya

