Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Jihar Gombe Tayi Fice A Bangaren Inganta Lafiya Matakin Farko
Published: December 14, 2025 at 3:50 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jihar Gombe ta yi fice a gasar kiwon lafiya a Matakin farko ta ƙasa ta 2025, ta lashe Dalar Amurka 400,000

Jihar Gombe ta sake tabbatar da jajircewarta wajen inganta harkar kiwon lafiya, inda ta samu matsayi na biyu a shiyyar Arewa Maso Gabas a gasar Jagorancin Kiwon Lafiya Matakin Farko (PHC Leadership Challenge) ta shekarar 2025, tana yin fintinkau kan jihohi shida na shiyyar.

Sakamakon wannan ƙwazon da Gombe ta nuna wajen ƙarfafa tsarin kiwon lafiyar farko, an karrama ta da kyautar dala 400,000.

An miƙa kyautar ne yayin bikin karramawa na 2025 PHC Leadership Challenge da aka gudanar a cibiyar taro ta Bola Ahmed Tinubu, dake Abuja.

Bikin ya samu halartar manyan jami’ai da masu ruwa da tsaki a fannin lafiya, inda mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya jagoranci taron.

A shekarar da ta gabata ma, jihar Gombe ta kafa tarihi inda ta lashe PHC Leadership Challenge Innovation Award, lambar yabo ta kirkira da aka fara bayarwa tun bayan ƙaddamar da shirin, kuma ta zama ta biyu a Arewa Maso Gabas, lamarin da ya kawo mata kyautar dala $400,000.

Wannan ci gaba ya sake tabbatar da cewa Gombe na kan gaba wajen inganta harkar kiwon lafiya na asali a Najeriya.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Gwamna Kefas Na Jihar Taraba Ya Karbi Shaidar Jam’iyar APC
Next Post: Hafsan Sojin Najeriya: Samar Da Sabbin Wajen Horas Da Sojoji Zai Inganta Tsaro

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Najeriya Tace Ta Farmaki Mayakan ISIS A Jihar Sokoto Labarai
Gwamnatin Kano Ta Rufe Gidajen Bukukuwa Da Shakatawa Labarai
Fadar Sarkin Musulmi: Talata Ne 1 Ga Watan Sha’aban Na 1447AH Najeriya
Sabunta Manhajar Ilimi A Duk Matakai Nasara Ce! Najeriya
An Gurfaranar Da Wadanda Ake Zargi Takai Hari Gaban Kotu Najeriya
Hukumar Zaben Najeriya Ta Sanar Da Ranar Zaben Shugaban Kasa Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Wani Ya Yiwa ‘Yar Sa Mai Shekaru 8 Fyade A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC Siyasa
  • Kasar Uganda Ta Tsare ‘Yan Jam’iyyun Adawa Dubu Biyu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Paparoma Leo: Zai Kai Ziyara Ƙasar Angola Labarai
  • Babban Sakataren MDD Yayi Allah Wadai Da Matakin Soja A Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Gwamna Ododo Ya Gargadi Sarakunan Gargajiya Najeriya
  • Kasashen Daular Larabawa Tare Da Saudiya Da Jordan Sunyi Allah Wadai Da kasar Israel Afrika
  • Mutane Kusan 30 Ne Suka Mutu a Nguru Dake Jihar Yobe Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.