Amurka ta yi tur da tsare wasu jami’an ta da kasar Afirka ta Kudu ta yi, wadanda aka ce su na aikin ba da tallafi ga turawan Afirka ta kudu jinsin Afrikaner.
Wani jami’in hukumar kula da shige da ficen baki ta Amurka ya fadawa kamfanin dillancin labaran reuters cewa an tsare wasu jami’an hukumar su biyu na wani dan lokaci, amma an kyale su a ranar talata.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ATK ta ce babu wani jami’in Amurka da aka kama a kasar.
Ranar laraba, hukumomin ATK sun ce sun kama, kuma zasu kori wasu ‘yan kasar Kenya su 7 da suke aiki ba tare da izni ba na taimakawa gwamnatin Amurka wajen tattara takardun neman yin kaura zuwa Amurka na turawan ATK.
Gwamnatin shugaba Donald Trump tana shirin bayar da mafaka ga dubban turawan ATK Amurka bisa hujjar cewa ana musgunawa ko cin zarafinsu don kawai su turawa ne a kasar, zargin da gwamnatin ATL ta ce babu ko kamshin gaskiya a cikinsa.


