Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15 Afrika
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe Afrika
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya Afrika
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu Kiwon Lafiya
  • NUJ Ta Kai Ziyarar Jaje GMC Bayan Gobara Ta Lalata Ginin Sashen Talabijin Afrika

Kasashen AES Sun Buɗe Gidan Talabijin Na Bai Daya
Published: December 22, 2025 at 12:32 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ƙasashen ƙungiyar AES, wato Burkina Faso da Mali da Nijar, sun buɗe gidan talabijin na bai ɗaya domin ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakaninsu, tare da isar da sahihan labarai ga al’ummomin ƙasashen uku.

Ministocin Harkokin Ƙasashen Waje na ƙasashen AES ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar buɗe gidan talabijin ɗin a ranar 21 ga Disamba, a babban birnin ƙasar Mali, Bamako.

A cewar ministocin, an kafa wannan gidan talabijin ne domin ya zama murya ta bai ɗaya ga ƙasashen, inda zai riƙa bayyana matsayinsu kan muhimman batutuwa da suka shafi siyasa, tsaro, tattalin arziki da ci gaban yankin Sahel.

Sun ƙara da cewa tashar za ta taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da yaɗa labaran ƙarya, da kuma kare al’adu, ɗabi’u da muradun al’ummomin ƙasashen uku.

Haka kuma, sun bayyana cewa gidan talabijin ɗin zai taimaka wajen kusantar da jama’a da gwamnatocinsu, tare da nuna nasarori da ƙalubalen da ƙasashen AES ke fuskanta.

Masu sharhi na ganin cewa buɗe wannan gidan talabijin wata babbar alama ce ta ƙudurin ƙasashen AES na dogaro da kansu a fannin yaɗa labarai da kuma ƙarfafa haɗin kai a yankin Sahel.

Afrika, Labarai

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Ranakun Hutu
Next Post: Gwamnatin Amurka Da Najeriya Sunyi Hadakar Inganta Asibiticin Kiristoci

Karin Labarai Masu Alaka

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Jama’ar Arewa Maso Gabas Afrika
Ganduje Ya Nisanta Kansa Da Batan Dadiyata Labarai
Gwamnatin Gombe Ta Kaddamar Da Sabon Ofishin GOGIS Don Inganta Tsarin Filaye Afrika
Harin Jirgi Marar Matuki Ya Kashe Kakakin ‘Yan Tawayen M23 Afrika
Hotunan Hawan Sallah A Masarautar Bauchi Afrika
Fargaba Ta Karu Duk Da Tsagaita Wuta Tsakanin Iran Da Amurka Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu
  • NUJ Ta Kai Ziyarar Jaje GMC Bayan Gobara Ta Lalata Ginin Sashen Talabijin

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ana Tuhumar Dan Shugaba Robert Magabe Da Kisan Kai Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Zata Farfado Da Cibiyar Koyon Sana’oi Ta Dangote Afrika
  • Netanyahu Yayi Gaggawar Amincewa Da Kasafin Kudin Kasar Afrika
  • Amurka Ta Daina Bawa Israila Bayanan Sirri Amurka
  • Sojoji Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda a Kukareta Afrika
  • Farmakin Da Aka Kai Makarantar Mata A Iran Yayi Ajalin Yara Da Dama Afrika
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Dan Hamayya Ya Amince Da Faduwa A Zaben Kasar Benin Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.