A halin da ake ciki, Kurdawan kasar Sham ko Syria, sun gargadi ‘yan’uwansu na kasar Iran da kada su yarda su kulla kawance da Amurka wajen yakar Gwamnatin Iran.
Kurdawan na kasar Syria sun yi misali da irin halin da suka samu kansu a ciki, suna masu fadin cewa za a yi amfani da su ne kawai a kasar.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters yace rundunonin sa kai na Kurdawan Iran dake zaune a yankin arewacin Iraqi, sun gana a lokuta da dama da wakilan Amurka a cikin ‘yan kwanakin nan a kan kai farmaki kan dakarun kasar Iran a yankin yammacin kasar, yayin da Amurka da Isra’ila ke kai hare-hare ta sama.
Amma Kurdawan Syria, wadanda suka yi kawance da Amurka sun ja kunnen ‘yan’uwansu na Iran cewa za a jefa su a rana, a bar su, kamar yadda Amurka ta yi ma Kurdawan na Syria.
Wani Bakurde mai shekaru 45 mazaunin garein Qamishli na Kurdawa a arewa maso gabashin Syria, ya jaddada gargadi ga Kurdawan Iran cewa kada su yi kuskuren da Kurdawan Syria suka yi.


