Jagoran Tafiyar Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bukaci Gwamna Abba K. Yusuf da ya bar kujerar gwamna idan har yana shirin ficewa daga jam’iyyar NNPP.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wani taro da magoya bayansa da masu ruwa da tsaki a Kano, a daidai lokacin da ake rade-radin cewa gwamnan na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Ya ce ba daidai ba ne a kwace wa tafiyar Kwankwasiyya kujerar gwamna daya tilo da take da shi a fadin Najeriya.
“Idan APC tana da kusan gwamnoni 30, me ya sa sai gwamnan Kano? Shi ne kadai ya rage mana,” in ji Kwankwaso, yana mai cewa duk wanda ke tursasa gwamnan ya sauya sheka ya kamata ya gaya masa ya bar kujerar gwamna ya tafi.
Tsohon gwamnan ya bayyana halin da ake ciki a siyasar Kano a matsayin abin tayar da hankali, yana mai gargadin cewa rikicin ba zai amfani jihar ba.
Ya ce yana kokarin sasanta al’amura a bayan fage domin hana jihar fadawa matsala.
Kwankwaso ya jaddada cewa gwamnatin NNPP har yanzu tana da lokaci ta yi wa al’umma aiki, yana mai kira da a hada kai maimakon rikici, sannan kuma yayi Suka game da kiran komawa abin da ya kira “Gandujiyya”, yana mai cewa hakan ya nuna rarrabuwar siyasa a jihar.
Ya karyata ikirarin cewa NNPP ba ta da karfi a Kano, yana mai cewa jam’iyyar ce mafi rinjaye.
Jagoran Jam’iyar ya gargadi shugabancin APC da kada su raina Kano, yana mai cewa jihar na da muhimmanci kuma ya kamata a rika mu’amala da ita cikin taka-tsantsan.


