Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Majalisar Dottijan Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Na’ura
Published: February 11, 2026 at 6:48 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ranar talata majalisar dattawan Najeriya ta amince da hukumar zabe ta tura sakamakon zabe nan take ta na’ura, mataki da a baya taki amincewa dashi, bayan da ta fuskanci matsin lamba daga kungiyoyin kwadago, kungiyoyin farar hula, da lauyoyi, wadanda suke kokarin ganin sun hana magudin zabe.

A makon jiya wakilan majalisar suka ki amincewa da umarnin a tura sakamakon zabe nan take bayan da aka kidaya kuri’u ta na’ura, mataki da ‘yan gwagwarmayar kawo sauyi a tafarkin zaben kasar suka jima suna goyon bayansa a zaman wata dama na hana yin shishshigi lokacin da ake tara kuri’u da kidaya su.

Matakin kin amincewa wannan kuduri da majalisar tayi da farko ya janyo mata suka tako ina, har ya sanya ‘yan Gwagwarmaya da shugabannin jam’iyun adawa suka yi zanga zanga ranar Litinin a harabar majalisar dokokin kasar, har suka bukaci majalisar dattawan ta bi sahun majalisar wakilai wacce tun farko ta amince da wannan mataki.

An jima ana zargin zabe a Najeriya yana cike da sayen kuri’u, tarzoma, da kuma rudani, inda daga karshe kotuna ne suke ayyana wanda ya sami nasara.

Kasar zata yi zabe ne cikin watan Feburairun shekara mai zuwa, inda ake sa ran shugaba Tinubu zai nemi wa’adi na biyu kuma na karshe.

Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Muna Kokarin Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Gombe – Uwargidan Gwamna
Next Post: Ethiopia Tana Horas Da Dakarun RSF A Wani Sansani

Karin Labarai Masu Alaka

Ruwan Sama Ya Dai-Daita ‘Yan Gudun Hijira A Gaza Labarai
Fiye Da Mutane 200 Sun Rasa Rayukansu A Wajen Hakar Ma’adanai Labarai
Kasar China Ta Sauka Daga Ragamar Bada Bashi Labarai
Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya Tayi Kakkausar Lafazi Game Da Harin Maiduguri Afrika
Gwamnan Jihar Gombe Ya Umurci A Rufe Makarantu Labarai
Kocin Zambia Na Mata Ba Lafiya Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Maka Wasu Jami’an Immigration A Kotu Bisa Zargin Rashin Da’a A Birtaniya Labarai
  • Gwamnatin Trump Tana Cigaba Da Korar Baki Daga Amurka Afrika
  • Dakarun Sojin Amurka Sunfara Sauka A Najeriya Amurka
  • Iran Zata Mayarwa Amurka Martani Amurka
  • Ana Cigaba Da Ceto Masunta Daga Ruwa A Ghana Labarai
  • Jihar Gombe Ta Saka Hannu Kan Yarjejeniya Da Kamfanonin Tunisiya Kimiya
  • Gwamnatin Tarayya: Bikin Al’adun Argungu Ya Karbu A Idon Duniya Labarai
  • Tattalin Arzikin Kasar Uganda Zai Bunkasa A Wannan Shekarar Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.