Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Majalisar Wakilai Tayi Allah Wadai Da Hare-Haren ‘Yan Bindiga A Gombe
Published: February 1, 2026 at 5:10 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Majalisar Wakilai ta yi Allah-wadai da munanan hare-haren ’yan bindiga a Gombe, ta nemi a ɗauki matakin soji cikin gaggawa.

Majalisar Wakilai ta amince da wani kudiri na gaggawa da ya shafi bukatun jama’a dangane da yawaitar hare-haren ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Akko ta jihar Gombe, waɗanda suka yi sanadin mutuwar akalla mutane shida, sace wasu 20, tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin naira.

Kudirin, wanda Usman Bello Kumo ya gabatar, ya jawo hankalin ’yan majalisar kan sabbin hare-hare da aka kai cikin tsari a Garin Galadima, Pindiga, Garin Jaji, Laro da sauran al’ummomin da ke kewaye, lamarin da ya haddasa fargaba mai tsanani, kauracewar mazauna yankunan daga gidajensu, da kuma asarar hanyoyin samun abin dogaro.

Yayin gabatar da kudirin a zaman majalisa a Abuja, Kumo ya bayyana cewa hare-haren sun tilasta wa mazauna yankunan da dama gudun hijira, lamarin da ya ƙara tsananta matsalolin jin ƙai da kuma tabarbarewar tsaro a yankunan da abin ya shafa.

Bayan amincewa da kudirin, Majalisar ta yanke shawarar kira ga Hukumar Kula da bayar da agajin gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da Hukumar Raya Arewa maso Gabas (NEDC) da su gaggauta samar da kayan agaji ga waɗanda abin ya shafa da kuma mutanen da suka rasa muhallan su a al’ummomin da abin ya shafa.

Haka kuma, ’yan majalisar sun yi kira ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya gaggauta umartar Babban Hafsan Tsaro da ya ƙaddamar da haɗaɗɗiyar rundunar tsaro domin korar ’yan bindigar da rushe sansanoninsu, tare da hana faruwar irin waɗannan hare-hare nan gaba.

Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Yanbindiga sun Kashe mutun guda tare da yin garkuwa da mutane kimanin 100 a Jihar Nejan Najeriya.
Next Post: Jami’ar Tarayya A Gombe Ta Karyata Harin ‘Yan Bindiga

Karin Labarai Masu Alaka

NDLEA Ta Fara Binciken Kwakwaf Akan Wasu ‘Yan Mata Dake Kai Kwaya Gidan Yari Labarai
Na Yi Murabus Ne Don Amurka Ta Keta Haddin Iraniyawa Amurka
Hawan Sallah A Jihar Katsina Afrika
Kasar Saudiya Zatayi Gwajin Noman Dabino A Kano Labarai
Za’a Ninka Shekarun Kurkuku Ga Masu Aikata Luwadi A Senegal Afrika
Gwamnatin Gombe Ta Dauki Sabbin Matakan Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Najeriya Zata Farfado Da Cibiyar Koyon Sana’oi Ta Dangote Afrika
  • Hukumar MDD Tace Wadanda Suka Mutu A Harin Sudan Sun Haura 70 Afrika
  • Gwamna Abba Gida-Gida Na Dari-Darin Shiga APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Yan Fashi Sun Shiga Gidan Alex Iwobi A Ingila Wasanni
  • Da Alamu Ronaldo Zai Buga Dukkan Wasanni Da Gasar Kofin Duniya A 2026 Wasanni
  • Gwamnonin Arewa Maso Yammacin Najeriya Sun Halarci Taron Inganta Makashi A Birnin Landan Afrika
  • Najeriya Da Amurka Sun Amince Su Haɗa Kai Don Inganta ’Yancin Addini Da ƙarfafa Tsaro A Nijeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Rundunar Operation Hadinkai Sunyi Nasara Akan ISWAP Da Boko Haram Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.