Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Iran Da Amurka Zasu Kulla Yarjejeniyar Nukiliya Amurka
  • Channels TV: Ta Yi Rashin Hazikin Dan Jarida Mr Khani Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Gano Gawar Dan Yawon Bude Ido A Kasar Chadi Afrika
  • Anyi Sallar Rokon Ruwa A Saudiya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaban Amurka Zai Sake Aika Jirgin Yaki Gabas Ta Tsakiya Amurka

Ministan Harkokin Wajen Iran Yagana Da Shugaban Sa’ido Akan Nukiliya
Published: February 16, 2026 at 6:29 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ministan harkokin wajen Iran ya gana da shugaban hukumar sa ido kan makamashin nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya a Ranar Litinin, kafin ci gaba da tattaunawa tsakanin Iran din da Amurka don shawo kan rikici game da makaman Nukiliya na Iran, inda alamu kadan ke nunawa za’a samu daidaito, ga kuma barazanar daukan matakin soja dake tunkarowa.

A makon da ya gabata ne, fadar Washington ta aike da jirgin ruwa mai dakon jiragen yaki a karo na biyu zuwa gabas ta tsakiya. Ita kuma kasar Iran a yau Litinin ta fara gabatar da atisayen soja a mashigar Hormuz, wanda gabar ruwa ne mai muhimmanci ga kasashen waje, kuma ta nan ake fitar da man fetur daga kasashen larabawa na tekun Fasha, wadanda suke ta rokon a bi hanyar diplomasiyya don kawo karshen rikicin.

Amurka da Iran sun sake zama don tattaunawa kan shirin Iran na nukiliya, wanda fadar Washington da sauran kasashen yamma ke ganin Iran na yi ne don gina makaman nukiliya. Abinda Iran din ta musanta.

Farashin man fetur bai samu wani sauyi mai yawa ba a ranar Litinin, yayin da masu sa hannun jari suke duba yadda tattaunawa tsakanin Iran da Amurka zata shafi kasuwar man, da kuma sa ran da ake na samun karuwar man daga kasashe masu arzikin man fetur na OPEC.

Afrika, Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: An Kama Masu Fasa Kaurin Gawayi A Malawi

Karin Labarai Masu Alaka

Iran Da Amurka Zasu Kulla Yarjejeniyar Nukiliya Amurka
Bincike Yanuna Kasashen Afirka Suna Cikin Mafiya Cin Bashi A Duniya Afrika
Yau Litinin Ake Cigaba Da Shari’ar Najib Zarak Labarai
Habasha Tafara Gina Filin Jirgin Sama Mafi Girma A Afirka Afrika
Anyi Rashin Mutane Da Yawa Yayinda Bom Ya Fashe Ana Sallar Magariba Maiduguri Labarai
Ansamu Girgizar Kasa A Kasar Taiwan Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ministan Harkokin Wajen Iran Yagana Da Shugaban Sa’ido Akan Nukiliya
  • An Kama Masu Fasa Kaurin Gawayi A Malawi
  • Rundunar Sojin Najeriya Ta Dakile Harin ‘Yan Ta’adda A Jihar Borno
  • Guguwa Mai Karfi Ta Raunata Dubban Mutane A Madagascar
  • Iran Da Amurka Zasu Kulla Yarjejeniyar Nukiliya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • An Maka Wasu Jami’an Immigration A Kotu Bisa Zargin Rashin Da’a A Birtaniya Labarai
  • Yanayin Sanyi Yayi Kamari a Yankin Gaza Tsaro
  • Ma’aikatan Tattara Kudin Haraji Sunyi Rikici Da Masu Babura A Bauchi Najeriya
  • Umar Aliyu, Shugaban Magoya Bayan Wikki Tourist
    Jagorancin Wikki Tourist FC Na Samun Yabo Wasanni
  • Kasar Zimbabwe Ta Samar Da Dokar Tsawaita Mulkin Mnangagwa Zuwa 2030 Labarai
  • Kasar Amurka Tabada Tabbacin Bawa Ukraine Tsaron Shekarun 15 Amurka
  • Tarayyar Turai Zasu Kirkiro Sojojin Haɗin Gwiwa Labarai
  • Ukraine Tana Cigaba Da Tattaunawa Da Amurka Domin Kawo Karshen Yakin Kasar Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.