Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u
Published: July 2, 2026 at 7:08 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci masu ruwa da tsaki a kamfanonin ɗab’i na Nijeriya da su rungumi haɗin kai, sasanci da haɗin gwiwa domin bunƙasa masana’antar tare da ƙara mata ƙarfin gogayya a matakin duniya.

Ministan ya yi wannan kiran ne a ranar Talata a wurin Babban Taron Masu Ruwa da Tsaki na Maɗaba’u na Nijeriya na shekarar 2026, wanda aka gudanar a otal ɗin Nicon Luxury da ke Abuja.

A cewar sa, warware rikicin shugabanci da ya daɗe a Cibiyar Ƙwararrun Maɗaba’u ta Nijeriya (CIPPON) ya samar da wata dama ta sake farfaɗo da masana’antar da kuma amfani da cikakkiyar damar tattalin arzikin ta.

Ya ce: “Tarihi ya ba ku dama ta sake gina wannan masana’anta. Don Allah ku yi amfani da ita, ku yi aiki tare, kuma kowa ya mara wa shugabanci baya domin ku ciyar da wannan sana’a gaba tare.”

Idris ya ce rikicin da ya daɗe yana addabar cibiyar yana daga cikin batutuwan farko da aka gabatar masa bayan ya kama aiki a matsayin minista, inda ya ƙara da cewa ya zaɓi sasanci da tattaunawa ne saboda ya yi imanin cewa hakan ya fi amfani fiye da doguwar shari’a.

Ya bayyana masana’antar ɗab’i a matsayin wata muhimmiyar hanya ta bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi, yana mai cewa idan masu ruwa da tsaki suka kasance tsintsiya maɗaurin ki ɗaya, masana’antar za ta fi samun goyon bayan gwamnati da manufofin da za su bunƙasa ta.

Ministan ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiki tare da CIPPON da sauran hukumomin da abin ya shafa domin ƙarfafa ƙa’idojin ƙwarewa, inganta yanayin gudanar da sana’ar da kuma ƙara gudunmawar masana’antar wajen cigaban ƙasa.

Haka kuma ya buƙaci shugabannin cibiyar da su bai wa kowa dama ba tare da la’akari da saɓanin da ya gabata ba, yana mai cewa shugabanci mai haɗa kowa ne zai samar da zaman lafiya mai ɗorewa da kuma kyakkyawan gado ga waɗanda za su zo nan gaba.

Ya kuma shawarci masu sana’ar ɗab’i da su rungumi sababbin fasahohi domin ci gaba da kasancewa masu tasiri a wannan zamani na fasahar dijital.

A nasa jawabin, Shugaban CIPPON kuma Shugaban Majalisar Gudanarwar ta, Koko T. Clement, ya ce cibiyar ta samu cigaba tun bayan rantsar da sabuwar majalisar gudanarwar ta a watan Disamba 2025.

Ya ce sun gudanar da tattaunawa da hukumomin gwamnati domin ƙarfafa ƙa’idojin ƙwarewar sana’a, inganta tsarin tafiyar da masana’antar da kuma samar da manufofin da za su taimaka wajen bunƙasa masana’antar ɗab’i a Nijeriya.

Ya ce: “Duk abin da muke yi domin cigaban wannan cibiya ne, domin amfanin kowane mai bugu, kowane ƙwararren mai aikin marufi, kuma kowane ɗan Nijeriya da ke dogaro da wannan masana’anta. Muna kira ga duk masu ruwa da tsaki da su yi aiki tare cikin zaman lafiya da fahimtar juna domin abin da ya haɗa mu ya kasance mafi girma fiye da duk wani abin da zai raba mu.”

Taron ya samu halartar shugabannin masana’antar ɗab’i, jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki, ciki har da Magatakardan CIPPON, Malam Abubakar Ndagi; Babban Jami’in Gudanarwa na KA2 Press Limited, Injiniya Michael Akinola; Daraktan Gudanarwa na kamfanin, Mista Ademola Kasumu da manyan jami’an Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, tare da sauran masu ruwa da tsaki daga masana’antar ɗab’i.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa
Next Post: Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ

Karin Labarai Masu Alaka

Ruwan Sama Ya Dai-Daita ‘Yan Gudun Hijira A Gaza Labarai
Amurka Ta Yi Juyin Mulki A Kasar Venezuela Amurka
Dakarun Pakistan Da Afghanistan Sunyi Arrangama Labarai
Akwai Yiwuwar Farashin Mai Zai Kara Tashi Afrika
Amurka Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasashe Hudu Domin Inganta Kiwon Lafiya Labarai
Harin Da Israela Ta Kai Gaza Yayi Ajalin Mutane 27 Da Yara Uku Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Farashin Kasuwar Yawon Bude Ido A Kasuwar Hannayen Jari Ya Fadi Afrika
  • Shugaban Amurka Donald Trump Ya Nanata Aniyar Mallakar Greeland Daga Kasar Denmark Amurka
  • Jami’an Tsaro Na Amfani Da Damar Su Wajen Cin Zarafin Jama’a Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa Afrika
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji A Jihar Kebbi Afrika
  • CAF Ta Fara Binciken Rikicin Bayan Wasa Tsakanin Algeria Da Najeriya Wasanni
  • An Bude Gasar Kwallon Kafa Ta Mata A Najeriya NWFL 2025 Wasanni
  • Amurka Ta Kakaba Takunkumi Ga Kwamandojin Yakin Kasar Sudan Sauran Duniya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.