Najeriya ta bada mafaka a ofishin jakadancinta ga wani dan hamayya a Guinea Bissau wanda yayi takarar shugaban kasa, mai suna Fernando Dias, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar. Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ne ta bayyana haka a yau Litinin.
Wannan ayyanawar tana zuwa ne a dai dai lokacin da shugabannin kungiyar ECOWAS, karkashin jagorancin shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio, suka yi kokarin shawo kan sojojin da suka yi juyin mulkin da su janye juyin mulkin.
A wani taro da aka yi yau Litnin, inda aka fusata kamar yadda wani ganau na Reuters ya tabbatar, jami’an ECOWAS sun nemi sojojin su bari a bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi, wanda ake gardama akai.
“ECOWAS ta bukaci da a dawo da tsarin demokuradiyya, da kuma ci gaba da tafiyar da harkokin zabe zuwa karshe,” inji ministan harkokin wajen Saliyo Musa Kabba.
Dan takarar shugaban kasar Dias mai shekaru 47 da haihuwa wanda sabon mutum ne a fagen siyasa, yace yana daf da lashen zaben kasar ne, sojoji suka yi juyin mulki a kasar.
Gungun jam’iyyun hamayya da suke goyon bayan Dias sun yi tur da juyin mulki, suna zargin tsohon shugaban kasar Embalo ne da hada baki da sojoji suka yi juyin mulki, don kada a bayyana sakamakon zaben.


