Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Za A Cigaba Da Tattaunawa Domin Kawo Karshen Yakin Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Najeriya Na ƙoƙarin Shiga Gasar Cin Kofin Duniya 2026 Ta Barauniyar Hanya
Published: January 22, 2026 at 6:24 AM | By: Bala Hassan | Updated: January 22, 2026

Tsohon kyaftin ɗin Super Eagles, na Najeriya Sunday Oliseh, ya yi iƙirarin cewa Najeriya na ƙoƙarin samun cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2026 ta wata hanya daban.

Oliseh ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake yi wa jaridar Sunday Oliseh ta Global Football Insights jawabi bayan kammala gasar AFCON ta 2025 a Morocco wadda Senegal ta lashe bayan ta doke ƙasar da ke karɓar baƙuncin gasar a wasan ƙarshe.

Tsohon dan wasan na Najeriya yace a tuna cewa Najeriya ta gaza samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya bayan ta sha kashi a hannun DR Congo a wasan ƙarshe na playoff a watan Nuwamba shekarar da ya gabata.

Mun kasa samun cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 a filin wasa, inda a zahiri yake da muhimmanci maimakon mu kalli abun ta hanyar suwaye suka ɗauki alhakin,” in ji Oliseh.

Waɗannan korafi da aka shigar wa hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, a kan DR Congo, shin ba mu fahimci abin da ke faruwa a nan ba?

“Mutane da yawa ba sa nuna yatsa ga waɗanda suka yi mana laifin gazawarmu; maimakon haka, suna zargin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta yi amfani da waɗannan ‘yan wasan a kan Kamaru kafin ma ta buga wasa da mu, kuma sun yi amfani da su a nan gasar AFCON ba tare da wata matsala ba.

“Muna ƙoƙarin cushe don shiga gasar cin kofin duniya ta hanyar ofis, maimakon ta hanyar samun nasara a filin wasa wajan cin kwallaye, dabaru da aiki tuƙuru wannan shine abunda muka gaza tun a farko. In ji Oliseh.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: Ana Sa Ran FIFA Za Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da Najeriya Ta Shigar Kan DR Congo
Next Post: Kungiyar Maharba Da ‘Yan Sintiri Sun Samu Kyautar Motoci

Karin Labarai Masu Alaka

CAF Ta Dakatar Da Kocin Senegal Pape Thiaw Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Najeriya Ta Mika Koke Ga FIFA Tana Zargin DR Congo Ta Sanya ‘Yan Wasan Da Basu Cancantaba Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Tabbas Za’a Gudanar Da Gasar Firimiya Lig Ta Najeriya Wasanni
Hawan Sallah A Jihar Katsina Afrika
CAF Ta Yanke Hukunci Kan Ƙasashen Senegal Da Moroko AFCON 2025 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
CAF, Zata Ci Tarar Wasu Kasashe AFCON 2025 Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 33 Bisa Zargin Kai Hari A Jihar Kwara
  • Papa Roma Leo Yayi Gargadi Game Da Rushewar Dimokraɗiyya
  • Jiragen Ruwa Suna Biyayya Ga Dokar Hana Ketare Ruwa
  • Gwamnatin Najeriya Tace A Maboyar ‘Yan Ta’adda Aka Kai Harin Jilli
  • Za A Cigaba Da Tattaunawa Domin Kawo Karshen Yakin Gabas Ta Tsakiya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Na Yi Murabus Ne Don Amurka Ta Keta Haddin Iraniyawa Amurka
  • Tabbas Za’a Gudanar Da Gasar Firimiya Lig Ta Najeriya Wasanni
  • Putin, Sakon Sabuwar Shekara Ya Jinjinawa Dakarun Rasha Da Suke Yaki A Ukraine Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Wani Jirgin Sama Ya Karya Dokar Hana Zirga Zirga Amurka
  • Ana Sa Ran FIFA Za Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da Najeriya Ta Shigar Kan DR Congo Wasanni
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • CAN: Da Alamu Daliban St. Mery Na Cikin Koshin Lafiya Najeriya
  • Za’a Gurfanar Da Sojojin Da Ake Zargi Da Yunkurin Juyin Mulki Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.