Prime Ministan Pakistan Shebbaz Shariff, ya fada ranar talata cewa a shirye yake ya zama mai masaukin baki a shawarwari tsakanin Amurka da Iran na kawo karshen yakin na yankin Gulf, kwana daya bayan da shugaban Amurka Donald Trump, ya dakatar da barazanar da yayi na kai hari kan cibiyoyin wutan lantarki na Iran, cewa an gudanar da shawarwari masu ma’ana.
Duk da haka, Amurka tana shirin tura dubban karin sojoji daga runduna ta 82 zuwa gabas ta tsakiya, kamar yadda mutane biyu da suke da masaniya dangane da batun suka shaidawa kamfanin dillancn labarai na Reuters. Kari kan tulin dakarun da ta aike yankin, wadda hakan yake kara janyo fargabar yakin zai dauki lokaci mai tsawo.
A rubutu da ya wallafa a shafin dandalin sada zumunta na X, PM Sharif yace, Pakistan tana maraba, kuma tana bada cikakken goyon baya kan kokari da ake yi na yin shawarwari domin kawo karshen yakin.
Ahalinda ake ciki kuma, rahotanni suka ce Iran ta tsananta matsayinta kan shawarwarin yayinda tayi ruwan makamai masu linzami kan Isra’ila, kasuwar hannayen jari a Amurka ta fadi kasa, saboda fargabar babu alamar kakkautawa a rikicin da ake yi a yankin.
A wata kuri’ar neman jin ra’ayin jama’a da kamfanin dillancin labarai na Reuters da IPSOS, suka gudanar, ya nuna farin jinin shugaban Amurka Donald Trump ya zube zuwa kashi 36 cikin dari matsaya mafi karanci tunda ya koma fadar White House, saboda karin farashin mai.


