Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Ranar Talata Amurka Da Isra’ila Sun Cigaban Da Kai Farmaki Iran
Published: March 11, 2026 at 4:19 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Amurka da Isra’ila sunyi luguden wuta kan Iran a jiya talata, da ma’aikatar tsaron Amurka da ake kira Pentagon da Farisawan suka ce shine hari mafi tsanani tun fara yakin, duk da tsammanin da kasuwannin sayar da hannayen jari na duniya suka yi cewa shugaba Donald Trump zai kawo karshen yakin bada jumawa ba.

Kara jawo kalubale ga tattalin arzikin duniya, rundunar juyin juya hali ta Iran tace zata hana jigilar mai daga yankin Gulf idan Amurka da Isra’ial basu tsaida kai mata hari ba.

Sakataren ma’aikatar Tsaron Amurka Pete Hegseth yace “yau zata kasance rana da muka fi tsananta kai hare hare a cikin Iran, jiragen yaki mafi yawa, tare da amfani da bayanan sirri mai inganci,” inji sakataren a wani taro da manema labarai.

Mazauna birnin Tehran da suka yi magana da kamfanin dilancin labarai na Reuters bisa sharadin ba za’a bayyana sunayen su ba, suka ce babu inda jiragen yakin suka bari a birnin Tehran. Tace sai ka dauka jahannama. Tace ‘yayanta har tsoron bacci suke yi.

Duk da haka, kalaman shugaba Trump ranar Litinin cewa, “kusan an kammala yakin,” masu zuba jari sunyi amannar yakin zai kare nan ba da jumawa ba, kamin kassarawar da aka yi wa jigilar makamashi ta durkusar da tattalin arzikin duniya.

Shugabannin Iran suna ci gaba da nuna turjiya ko a yau talata. “Hakika bama neman a tsagaita wuta, mun hakikance cewa tilas a kwabi bakin mai tsaukana, saboda su koyi darasi, har abada ba za su kaiwa Iran hari ba, inji a kakakin majaisar dokokin kasar, Mohammmed Baqer Qalibaf, a shafinsa na X.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Shugaba Putin Ya Bukaci Kawo Karshen Yaki Da Iran
Next Post: Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Yace Rasha Tana Cin Ribar Yakin Gabas Ta Tsakiya

Karin Labarai Masu Alaka

Najeriya: Ba Don Leken Asiri Muka Tura Jirgin Yakin Mu Ba Afrika
Gwamnatin Najeriya Tana Saka Ido Akan Matsalolin Gabas Ta Tsakiya Afrika
Kasar Sham Ta Sallami Wasu Fararen Hula Labarai
Kasar Afirka Ta Kudu Ta Tsare Wasu Amurkawa Amurka
Anfara Kirga Kuri’a A zaben Kasar Guinea Labarai
An Kubutar Da Wani Wanda Mahaifinsa Ya daure Da Sarka Tsawon Shekaru 17 A Bauchi Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sabunta Manhajar Ilimi A Duk Matakai Nasara Ce! Najeriya
  • Kasashen Turai: Bazamu Yarda Da Dokar Harajin Trump Ba Labarai
  • Sojojin Kasar Isra’ila Sun Kashe Wani Babban Kwamandan Hamas Labarai
  • Babban Hafsan Sojan Libya Ya Mutu A Wani Hatsarin Jirgin Saman Turkiyya Afrika
  • Masu Hakar Ma’adanai 37 Sun Mutu A Jihar Filato Bidiyo
  • Isra’ila Ta Cire Sunayen Wasu Mutane Biyu Cikin Wadanda Take Fako Afrika
  • Trump Zai Sasanta Tsakanin Masar Da Habasha Amurka
  • Amurka Ta Kwace Jirgin Mai Mallakar Rasha Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.