Senegal ta lashe gasar cin kofin kasashen nahiyar afirka Afcon na shekarar 2025.
A ranar Lahadi 18/01/2026 an fafata a wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Afirka wadda ya guda a Kasar Moroko.
Senegal ce ta lashe gasar akan masu masaukin baki kasar Moroko da ci 1-0 bayan da akwa kwashe mintoci 120, ana fafatawa.

Pape Gueye ne ya jifa kwallo daya tilo da ta ba Senegal nasara a cikin mintuna na 94, cikin karin lokaci na minti 15 din farko (Extra time).
A lokacin da ake cikin wasan Senegal ta fice daga filin wasa saboda rashin amincewa da bugun daga kai sai maitsaron raga da aka ba wa Moroko a ƙarshen mintuna 90 din farko bayan da da alkalin wasa ya duba na’ura mataimakawa alkalin wasa na VAR an kwashe tsawon minti 14 kafin daga bisani Senegal ta dawo, aka buga sai dai Ibrahim Diaz, ya zubar da fenaretin bayan da mai tsaron ragar Senegal Mendy ya cafke da hannunsa.

An bada manyan kyautuktuka guda uku Brahim Diaz dan wasan Moroko ya lashe kyautar wadda ya fi zura ƙwallo a gasar ta Afcon.
Sai mai tsaron ragar Moroko Yassine Bounou, shi ne mai tsaron raga mafi hazaka.
Dan wasan Senegal Sadio Mane shi ne ɗan wasa mafi kwazo a gasar afcon ta bana.

Shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta Duniya Fifa Gianni Infantino ne ya miƙa kofin na Afcon wa Sadio Mane.
Kalidou Koulibaly ne kyaftin din Senegal sai dai bai buga wasan karshen ba saboda an dakatar da shi, amma ya zo wurin mika kofi sanye da kayan wasan Senegal.

Yayin da ‘yan wasan Senegal suke murnan lashe gasar sukuwa wasu da cikin yan wasan Moroko an hangosu suna ta sharban kuka ne bayan tashi a wasan.


