Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Shugaba Tinubu Ya Umurci Janyewa Manyan Mutane ‘Yan Sanda
Published: November 24, 2025 at 3:36 AM | By: Nasiru Adamu Elhikaya | Updated: November 24, 2025

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ba da umurnin janye jami’an ‘yan sanda masu tsaron lafiyar manyan mutane ko wasu kusoshi na gwamnati.

A taro na musamman da babban sufeton ‘yan sanda IGP Kayode Egbetokun, manyan hafsoshin soja da daraktan jami’an tsaron farin kaya DSS, shugaban ya ce duk mai bukatar jami’ai masu damara don kare lafiyarsa sai ya rubuta bukata ga hukumar jami’an tsaron farar hula SIBIL DIFENS don samun masu kariyar.

Taron da ya gudana a fadar Aso Rock na da zummar samarda mafita ga kalubalen tsaro da kuma ceto matan makaranta da a ka sace a jihar Kebbi.

Shugaba Tinubu ya nuna damuwar yanda a ke samun karancin jami’an ‘yan sanda a yankunan karkara don tura dimbin jami’an ga manyan mutane da hakan ke haddasa karancinsu a aiyukan da ya dace su fi maida hankali a kai.

Sanarwa daga kakakin shugaban Bayo Onanuga ta ce shugaban ya ba da umurnin daukar sabbin jami’an ‘yan sanda 30,000 don kara yawan jami’an da yawansu bai kai bukatar da a ke da ita a samarda tsaro ba.

 

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Ga Fili Ga Doki
Next Post: Malami: Gwamnatin APC Ta Gaza – “Yan-Kasa Kuwa Na Da Katin Zabe”

Karin Labarai Masu Alaka

Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Ya Zamo Khalifan Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Nnamdi Kanu Zai Daukaka Kara Har Zuwa Kotun Koli Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gwamna Abba Kabir Ya Hana Yunkurin Kafa Sabuwar Hisba A Kano Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Samar Da Tsaro A Jihar Kano Ba Sai An Sa Siyasa Ba! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Sako Ɗaliban Makaranta 130 Da Aka Sace A Jihar Neja  Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Amurka Ta Yi Juyin Mulki A Kasar Venezuela Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Babban Hafsan Sojan Libya Ya Mutu A Wani Hatsarin Jirgin Saman Turkiyya Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Na Shirin Yin Zamiya Don Biyan Bashi Labarai
  • An Kai Hari Kan Masu Hakar Ma’adanai A Kasar Mali Tsaro
  • Chelsea Tayi Kaca-Kaca Da Barcelona A Gasar UCL Wasanni
  • Jamhuriyar Congo Zata Cigaba Da Fitar Da Ma’adanai Afrika
  • Abun Da Kuke Buƙatar Sani Game Da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka 2025 Wasanni
  • Yarjejeniyar Britaniya Da Mauritius Kan Tsibiran Chagos Cin Zarafi Ne Labarai
  • An Bude Gasar Kwallon Kafa Ta Mata A Najeriya NWFL 2025 Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.