Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ranar Litinin yace, sashen leken asiri na sojojin kasarsa tana da shaida babu kokonto cewa Rasha tana ci gaba da baiwa Iran bayanan sirri, kuma yin haka inji zalensky, zai sa a dade ana yakin na gabas ta tsakiya.
“Wannan mataki a fili ba zai haifar da da mai ido ba, kuma tilas a tsaida shi, domin zai yi ta haddasa barna ne kawai. Hakkin ko wace kasa wacce ta san ciwon kanta ne, na tabbatar da ganin tsaro da kare barkewar manyan fitina, inji shugaba Zelensky.
“Tuni kasuwannin saye da sayar da hannayen jari suka nuna rashin gamsuwa, kuma hakan yana shafar harkar makamashi a ko wace kasa. Ta wajen taimakawa gwamnatin Iran ta dore da kuma auna haren haren da take kaiwa, Rasha tana taimkawa wajen ganin yakin ya dore.
A makon jiya fadar Kremlin tayi watsi da wani rahoto da jaridar Wall Street Journal ta wallafa cewa, Rasha tana samarwa Iran bayanai daga tauraron dan adam, da kuma fasahar jirgin drones mai inganci, zaman kanzon kurege.
Wani babban jami’in difilomasiyya kasar Ukraine, ranar Litinin, yace jigilar jiragen Drones zuwa Iran da Rasha take yi, ya halatta a kai hari a cibiyoyin kera wadannan jirage a Rasha, daga nan yayi kira ga kasashen yammacin duniya da su samarwa Ukraine makamai da zasu kai inda Rasha take kera wadannan jirage.


