Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Shugabannin Kasar Australia Sun Bukaci ‘Yan Kasar Suyi Zanga Zanga Cikin Lumana
Published: February 11, 2026 at 7:22 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: February 11, 2026

Ranar Talata Shugabanni a kasar Australia sunyi kira ga jama’a da su kai zuciya nesa, tare da kiran a gudanar da zanga zanga a cikin lumana, bayan da arangama ta barke a birnin Sydney, tsakanin ‘Yan sanda da masu zanga zangar nuna adawa da ziyarar da shugaban Isra’ila Isaac Herzog ya kai kasar.

‘Yan sandan kasar suka ce sun kama mutane 27 ciki harda mutum 10 kan zargin cin zarafin ‘yansanda, sakamkon tarzomar da ta barke lokacin da suka dauki matakin tarwatsa mutane da suka hallara a kusa da babban dakin taro dake birnin.

Masu zanga zanga ciki harda wata ‘yar majalisar dokokin kasar daga bangaren ‘yan hamayya, sun fada cewa ‘yansanda sun ci zarafin su.

PM kasar Anthony Albanese, yace yayi takaicin tarzomar, daga nan yayi kira ga masu zanga zanga su gudanar dashi cikin lumana.

“Yan kasar Australia suna bukatar abu biyu. Ba sa son ganin an kawo rigima anan. Suna son ganin an daina kashe mutane ko Isra’ila ce take yi ko Falasdinawa, amma basa son ganin an kawo fitina anan,” PM Albanese ya gayawa wata tashar rediyon kasar Triple M.

A cikin sanarwar da ‘Yansanda suka bayar, suka ce babu rahoton an sami jikkata mai tsanani a arangamar.

Afrika, Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Shugaban Afrika Ta Kudu Yanuna Goyon Bayan Kawo Karshen Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine
Next Post: Indonesia Zata Kafafa Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Gaza

Karin Labarai Masu Alaka

An Yanke Hukuncin Kisa Ga Hasina Tsohuwar Firaiy-Ministan Bangladash Labarai
Rikici Ya Lafa A Kasar Iran Bayan Daukar Matakai Labarai
An Damke Matasa Masu Gurza Kudaden Ketare Na Jabu Afrika
Mayakan RSF A Sudan Suna Sace Kananan Yara A Lokacin Yake-Yaken Kasar Afrika
Domin Inganta Tsaro Najeriya Ta Sayi Jiragen Yaki A Kasar Italiya Tsaro
An Kashe Sojojin Bangladesh A Kasar Sudan Tsaro

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Musa: “Da Yaddar Allah Zamu Ga Bayan Ta’addanci A Najeriya” Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Dan Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Atiku Abubakar Ya Shiga Jam’iyyar APC Siyasa
  • Ministan Kudin Botswana Yace Akwai Hasashen Cewa Tattalin Arzikin Kasar Zai Ragu Amurka
  • Dalibin Jami’a Ya Rasa Ransa A Birnin Dakar Yayin Zanga Zanga Afrika
  • Hukumar Zabe A Kasar Honduras Ta Sanar Da Nasry Asfura A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Ƙasa Afrika
  • An Samar Da Dala Kusan Biliyan Biyu Don Yakar Polio Labarai
  • An Kaiwa Sojojin Ghana Hari A Lebanon Afrika
  • Gwamnonin Arewa Maso Yammacin Najeriya Sun Halarci Taron Inganta Makashi A Birnin Landan Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.