Shugabar kungiyar cinikayya ta duniya Ngozi Okonjo Iweala, tayi kira ga kasashe a jiya Alhamis da su kawo gyare gyare a dokokin cinikayya ta duniya, inda tace yadda ake gudanar da abubuwa a da ya shude, biyo bayan shekara me cike da hargitsi da aka shiga sakamakon harajin kayan fito da Amurka ta kakaba, da kuma rikicin kasa da kasa.
A farkon wata ganawa ta ‘yan kungiyar da za’a shafe kwanaki hudu ana yi a kasar Cameroon, shugabar ta zayyana matsalolin da kungiyar ke fuskanta, ciki har da rashin kuzarin tsarin sulhunta rikici na kungiyar. Ta ce yadda ake aiwatar da abubuwa da muka sani yanzu ya sauya, sauyin da ba zai taba komawa irin na da ba, dole muyi hangen gaba.
Wasu jakadu da Jami’an cinikayya sun yi gargadin cewa idan ba’a cimma yarjejeniya kan kawo gyare-gyare ba, kasashe zasu fara watsi da dokokin cinikayya na duniya su kafa nasu dokokin.
Taron da ake gabatarwa a Younde, babban birnin Cameroon ya zo ne ana tsaka da damuwa kan abinda yakin da Amurka da Isra’ila suke yi da Iran, kuma ya biyo bayan shafe shekaru ba tare da cimma yarjejeniya kan cinikayyar kasa da kasa


