Rundunar Sojan Najeriya ta ce jiragen yaƙinta sun hallaka akalla ’yan bindiga 23 da ke tserewa daga jihar Kano zuwa jihar Katsina, a wani samame na haɗin gwiwa karkashin Operation Fansan Yamma.
A cewar rundunar, samamen ya biyo bayan wani hari da ake zargin ’yan bindiga sun kai a daren 1 zuwa safiyar 2 ga Janairu, 2026, a ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa na Jihar Kano.
Dakarun haɗin gwiwa da ke Kano sun dakile harin cikin gaggawa tare da yi wa ’yan ta’addan mummunar ɓarna, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa jihar Katsina, Sojojin sun bi sahunsu har zuwa ƙauyen Karaɗuwa da ke Ƙaramar Hukumar Matazu.
A wata sanarwa da Mai Taimaka wa Daraktan Hulɗa da Jama’a na Birgediya na 3, Major Babatunde Zubairu, ya fitar, ya ce bayanan leƙen asiri sun nuna cewa ’yan bindigar suna gudanar da jana’izar abokansu da aka kashe a yankin Ɗan Marke, a Ƙaramar Hukumar Matazu, lokacin da dakarun sama suka ga motsinsu.
Sanarwar ta ce an ci gaba da bibiyar su har sai da suka haɗu da baburansu bayan sun ƙetare wani busasshen kwarin rafi, inda jiragen yaƙin sama suka kai musu luguden wuta.
Rundunar ta bayyana cewa an hallaka akalla ’yan ta’adda 23, yayin da ake kyautata zaton wasu da dama sun samu raunuka kuma harin ya kuma lalata makamai da kayan aiki da dama na ’yan bindigar.
Kwamandan Birgediya na 3 ya yaba da jarumtaka da jajircewar dakarun sama da na ƙasa, yana mai cewa sun nuna bajinta na musamman a fagen yaƙi.
Rundunar Soja ta tabbatar wa al’ummar jihar Kano cewa yankin na ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali, tare da ci gaba da sintiri da sa ido a kai a kai.
Ta kuma gode wa jama’a bisa goyon bayan da suke bayarwa a yaƙi da ’yan ta’adda, tare da kiran su da su ci gaba da samar da bayanai cikin lokaci domin taimaka wa jami’an tsaro wajen dakile ayyukan ta’addanci.


