Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Mayakan RSF A Sudan Suna Sace Kananan Yara A Lokacin Yake-Yaken Kasar
Published: January 30, 2026 at 8:05 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 31, 2026

Wani bincike da kamfanin dillacin labarai na Reutres ya yi, ya bankado cewa Sojojin sa kai a Sudan sun sace yara lokacin da suka kwaci birnin al-Fashir a watan Octoba, da kuma lokacin da suka kai hare-hare a yankin na Darfur tun fara yakin basasar da ake ta gwabzawa tsakanin su da sojin kasar. An ce ma wani sa’in suna kashe iyayen yaran ne kafin su dauke su.

Wadanda abun ya faru a kan idon su sun shaidawa kamfanin dillacin Labarai na Reuters cewa, dakarun tawayen RSF sun fadawa iyayen yaran cewa za’a yi amfani da su ne a matsayin bayi don su yi kiwon dabbobi.

Rigima ta kaure ne tsakanin dakarun na RSF da sojojin Sudan tun watan Aprilun shekara ta 2023, kan wanda ya cancanta ya rike ragamar mulkin kasar msi arzikin albarkatu da yalwar kasar noma da kuma tasoshin jiragen ruwa a gabar da kogin bahar maliya.

Duk da cewa masu rajin kare hakki sun bada rahoton cewa duka bangarorin sun tafka laifukan yaki, ciki har da daukan yara don aiki a wajen daga, ba’a kawo rahoto kan sacewa da bautar da yara da kungiyar RSF da ‘yan kawancen ta ke yi ba.

Mutane 26 da abin ya faru a kan idon su, sun zanta da kamfanin dillacin labarai na Reuters ido da ido ko ta wayar tarho, bayan da suka tsere zuwa garin Tawila da ke arewacin Dafur ko kasar Chad. Sun yi bayanin abubuwan da suka faru, inda aka sace kalla yara 56 da shekarun su ya kama daga wata 2 zuwa shekara 17 tun a shekarar 2023.

Afrika, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Kungiyar ISIS Ta Dauki Alhakin Harin Kasar Nijar
Next Post: Tattalin Arzikin Kasar Uganda Zai Bunkasa A Wannan Shekarar

Karin Labarai Masu Alaka

Dillalan Mai Suna Fuskantar Karancin Mai Sakamakon Yakin Amurka Da Iran Afrika
Shugaban Amurka Yayi Watsi Da Tattaunawar Kawo Karshen Yaki Da Iran Afrika
Kasar Israela Zata Gina Sansani A Gaza Afrika
Kasar Gabon Ta Nemi Tallafin Asusun Bada Lamuni Na IMF Afrika
Afirka Ta Kudu Ta Bukaci Jakadan Israela Ya Fice Daga Kasar Afrika
Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha: Tura Sojojin Birtaniya Ukraine Zai Kara Ta’azzara Yaki Labarai
  • Rwanda Tana Keta Yarjejeniyar Zaman Lafiya – Tshisekedi Labarai
  • Najeriya, Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Sama Da 80, Sun Ceto 34 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Yagana Da Shugaban Sa’ido Akan Nukiliya Afrika
  • Amurka Ta Gabatarwa Sassan Dake Yakar Juna A Sudan da Shirin Tsagaita Wuta Afrika
  • Sojojin Isra’ila Sun Kashe Babban Kwamandan Kungiyar Hezbollah Afrika
  • Mala Buni: Zai Jagoranci Kwamitin Sassanci Na Jam’iyar APC Labarai
  • Masana: ‘Yancin Kasashen Afrika A Rubuce Yake Ba A Zahirance Ba Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.