Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

‘Yan Jarida Sunyi Mummunan Hatsari A Bauchi
Published: February 6, 2026 at 12:57 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: February 6, 2026

Daga Ahmad Muhammad,Bauchi

‘Yan jarida kimanin su 14 da suka fito daga kafafen yada labarai dabam -dabam suka gamu da mummunar hatsarin mota a yayin da suke cikin tawagar hukumar raya yankin Arewa Maso Gabas (NEDC)

Shugaban kungiyar Yan Jarida Na kasa reshen jihar Bauchi da ke Arewa maso gabashin Najeriya Kwamred Umar Said ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Umar Said wanda yake jagorantan aikin  yace tare suke tafiya , direban motar Yana gudu Sai taqwace ta Tashi sama ta shiga daji kafin daga bisani tayi ta dungure dasu tana zubar da mutanen da ke ciki har Allah ya tsaida su.

Ya nuna godiya wa Allah saboda ba a rasa rai ko daya ba a ciki amma an Samu munanan raunuka da asarar kayayyakin Aiki”

Ya godewa Ministan Uba Maigari Ahmadu , da Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi Muhammadu Awwal Jatau, da Shugaba da Manajin Darektan Hukumar NEDC sauran Ma’aikatan Hukumar da ‘Yanjaridu saboda yadda suka nuna damuwarsu kan abinda ya faru da Kuma yadda suka tsaya Kan lamarin.

Lokacin da abin ya faru Yan jaridun suna tafiya ne a ƙarƙashin jagorancin ƙaramin ministan raya yankuna, Alhaji Uba Maigari Ahmadu a yayin da suke yawon buɗewa da miƙa ayyukan da hukumar NEDC ta gudanar a jihar Bauchi zuwa hannun gwamnatin jihar.

Hatsarin ya faru ne a kan titin Yashi zuwa Yelwan Duguri da ke cikin ƙaramar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi da ke tarayyar Najeriya a yau ranar Jumma’a, bayan ministan ya qaddamar da katafaren makaranta a garin Yalwan Duguri.

‘yan jaridun sun samu munanan raunuka raunuka daban-daban yayin da ake ƙoƙarin samar musu da agajin gaggawa a asibitin Yelwan Duguri daga bisani kuma za a wuce da su babban asibiti a Bauchi domin neman musu kulawar likitoci.

‘Yan jaridun da abin ya Shafa waɗanda suka fito daga gidajen talabijin na Channels, AIT, NTA, BATV,Arise da wasu irin su wakilan manyan jaridun na Guardian, the nation, kamfanin dillancin labarai Na Nijeriya (News agency of Nigeria) (NAN) da sauransu da dama.

Hatsarin ya faru ne jimkaɗan bayan da tawagar suka buɗe aikin makarantar GSS a Yelwan Duguri inda suke kan hanyarsu ta zuwa domin buɗe wasu ayyukan.

Daga cikin waɗanda suke cikin tawagar har da minista, shugabannin NEDC, chairman da MD, mataimakin gwamnan jihar Bauchi da sauransu.

Kazalika, Wakilinmu wanda ke cikin tawagar ya shaida mana cewa motar da ta gamu da hatsarin ɗaya ce daga cikin motocin da ‘yan jaridan ke amfani da su a yayin aikin ɗauko labarin. Ya kuma tabbatar mana da cewa kayayyakin aikin jarida dama kamar su Kamarori sun lalace. Amma Babu asarar rai.

Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Jakadan Amurka A Poland Ya Yanke Hulda Da Kakakin Majalisar Kasar
Next Post: Tawagar Shirya Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe Ta Ziyarci Masarautun Jihar

Karin Labarai Masu Alaka

Tinubu: Ku Guji Yi Wadaka Da Kudin Kananan Hukumomi Najeriya
An Zargi Babban Mai Gabatar Da Kara A Kotun Duniya Ta ICC Afrika
Jirgin Sama Ya Fadi A Kano Labarai
Amurka Zata Kara Tura Sojoji Gabas Ta Tsakiya Afrika
Rundunar Sojin Najeriya Ta Dakile Harin ‘Yan Ta’adda A Jihar Borno Labarai
Guguwa Mai Karfi Ta Raunata Dubban Mutane A Madagascar Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ansamu Girgizar Kasa A Kasar Taiwan Labarai
  • Tinubu Ya Buƙaci Gwamnoni Su Mutunta Hukuncin Kotun Ƙoli Kan ’Yancin Kuɗin ƙananan Hukumomi Labarai
  • Najeriya: Ta Aiwatar Da Tsarin Ba Aiki Ba Albashi Ga Ma’aikata Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Na Duke Tsohon Ciniki Shirye-Shirye
  • Jiragen Saman Yakin Najeriya Suka Gurgunta Yunkurin Juyin Mulki A Benin Afrika
  • Kungiyar ISIS Ta Kashe Sojojin Amurka Biyu Amurka
  • Aisha Buhari Ta Bayyana Irin Kalubalen Da Ta Fiskanta Sakamakon Biyewa Jita-Jita Labarai
  • Kasar Ukraine Tayi Watsi Da Shiga Kungiyar NATO Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.