Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15 Afrika
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe Afrika
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya Afrika
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu Kiwon Lafiya
  • NUJ Ta Kai Ziyarar Jaje GMC Bayan Gobara Ta Lalata Ginin Sashen Talabijin Afrika

Tinubu, Akpabio da Ministoci 9 Zasu Tafi Ƙasar Birtaniya
Published: March 17, 2026 at 10:09 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja ranar Talata domin kai ziyara ta ƙasa zuwa Kasar Burtaniya a matsayin baƙon King Charles III da Sarauniya Queen Camilla.

Sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce Tinubu zai je tare da Uwargidan sa, Oluremi Tinubu, inda za a karɓe su a Windsor Castle daga 18 zuwa 19 ga Maris.

Rahoton ya ce wannan ita ce ziyara ta farko da shugaban Najeriya zai kai Birtaniya cikin shekaru 37, kuma za ta mayar da hankali kan ƙarfafa alaƙar ƙasashen biyu a fannoni kamar na kasuwanci, zuba jari, tsaro da musayar al’adu.

A yayin ziyarar, Tinubu zai kuma gana da Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, a 10 Downing Street, inda ake sa ran za a rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da dama tsakanin ƙasashen biyu.

Ana sa ran Shugaban Ƙasar zai dawo Najeriya bayan kammala ziyarar.

Afrika, Labarai, Najeriya, Nishadi

Post navigation

Previous Post: Tinubu Ya Aika Manyan Hafsoshin Tsaro Borno
Next Post: Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya Tayi Kakkausar Lafazi Game Da Harin Maiduguri

Karin Labarai Masu Alaka

Jami’ar Tarayya A Gombe Ta Karyata Harin ‘Yan Bindiga Najeriya
NAHCON Ta Fara Shirye-shiryen Dawowar Alhazai Afrika
Shugaba Tinubu: Naji Dadin Sako Daliban Neja Da Aka Sace Labarai
Gwamnatin Najeriya Zata Samar Da Sabbin Dakunan Karatun Dalibai Afrika
Gwamnatin Sokoto Tabada Umarnin Biyan Albashin Watan Fabrairu Labarai
Tinubu: Ku Guji Yi Wadaka Da Kudin Kananan Hukumomi Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu
  • NUJ Ta Kai Ziyarar Jaje GMC Bayan Gobara Ta Lalata Ginin Sashen Talabijin

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Zabebben Shugaban Hungary Yace Zaidawo Da Tsarin Dimokraɗiyya Afrika
  • Manoma Suna Fuskantar Barazanar Karyewa A Kasar Ghana Afrika
  • Shugaban Amurka Donald Trump Yace Amurka Zata Kai Babban Farmaki Iran Afrika
  • An tura tsohon ministan Ilimin Nijar gidan yari saboda zargin aikata fyade ga wata daliba. Afrika
  • Sabuwar Shekarar Musulunci: Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Yi Kira Da A Yawaita Addu’o’i Da Haɗin Kai Afrika
  • Abun Da Kuke Buƙatar Sani Game Da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka 2025 Wasanni
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Asabar 11.22.2025 Rediyo
  • RSF Ta Nemi A Gaggauta Gano Dan Jarida Moussa Kaka Da Ya Bace A Yamai Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.