Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna Afrika
  • Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi Afrika
  • Maulidin 2026: IMC Ta Yi Kira Da Ƙarfafa Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Najeriya Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Taya Sarkin Musulmi Murnar Cika Shekaru 70, Ya Yi Masa Addu’ar Ƙarin Lafiya Da Tsawon Rai Afrika
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika

Tinubu Ya Kawo Ƙarshen Aikin Kwamitin Sayar Da Kaddarorin Gwamnati
Published: July 30, 2026 at 8:21 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da rushe Kwamitin Shugaban Ƙasa mai kula da aiwatar da harkokin sayar da kaddarorin Gwamnatin Tarayya (Presidential Implementation Committee – PIC), tare da ba da umarnin aiwatar da matakin nan take.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, inda ya bayyana cewa daga yanzu dukkan harkokin da suka shafi ayyukan kwamitin za su koma ƙarƙashin kulawar Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi.

Sanarwar ta tuna cewa an kafa kwamitin ne a shekarar 2000, a zamanin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, domin kula da sayarwa da bayar da hayar filaye da sauran kaddarorin Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin tsarin Monetisation Policy.

Ta ce bayan nazari mai zurfi, Gwamnatin Tarayya ta gano cewa ayyukan kwamitin sun kauce daga ainihin manufar da aka kafa shi domin aiwatarwa, lamarin da ya janyo ƙararraki masu yawa a kotuna a sassan ƙasar nan.

A sakamakon haka, gwamnatin ta yanke hukuncin cewa babu wata buƙatar ci gaba da wanzuwar kwamitin.

Saboda haka, Shugaba Tinubu ya umarci a rushe kwamitin daga ranar 5 ga Nuwamban 2025, tare da ɗora wa Babban Lauyan Tarayya alhakin kula da dukkan harkokin da suka shafi ayyukan kwamitin.

Haka kuma, Shugaban Ƙasar ya umarci tsohon Sakataren kwamitin, B. S. Dutsin-Ma, da ya dakatar da duk wani aiki ko wakilci da yake yi a madadin kwamitin ko Gwamnatin Tarayya kan duk wani lamari da ya shafi ayyukansa.

Sanarwar ta ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na inganta yadda ake tafiyar da harkokin kadarorin gwamnati cikin tsari, gaskiya da inganci.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i, Sauran Duniya, Shirye-Shirye, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Haɗin Gwiwar GOSERC Da Savannah Zai Ƙarfafa Rarraba Wutar Lantarki A Faɗin Jihar Gombe
Next Post: Gwamnatin Najeriya Ta Jaddada Aniyarta Ta Daƙile Yaɗuwar Makamai Ba Bisa Ƙa’ida Ba

Karin Labarai Masu Alaka

Sakataren Kungiyar NATO Yayi Magana Da Hukumomin Kasashe Afrika
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane A Kauyuka Dake Yammacin A Najeriya Najeriya
Gwamnatin Tinubu Ta Karyata Kafa Kamfanin Gwal A Legas Labarai
Farashin Danyen Mai Ya Fadi A Kasuwar Duniya Afrika
Najeriya: Ta Aiwatar Da Tsarin Ba Aiki Ba Albashi Ga Ma’aikata Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugaban Amurka Ya Ya Bukaci Iran Ta Mika Wuya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Fanny Amun Ya Yi Murabus A Matsayin Shugaban Kwamitin Binciken NFF
  • Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna
  • Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi
  • Ceferin Ya Ce Ba Zai Yi Takarar Shugabancin FIFA Ba
  • Maulidin 2026: IMC Ta Yi Kira Da Ƙarfafa Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Najeriya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Nnamdi Kanu Ya Nemi A Mayar Da Shi Abuja Daga Gidan Yarin Sokoto Labarai
  • Menene Illar Yada Labaran Karya A Kafofin Sada Zumunta Na Zamani Labarai
  • Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Yace Rasha Tana Cin Ribar Yakin Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Hawan Sallah A Jihar Katsina Afrika
  • An Tura Rundunar Tsaron Sham Zuwa Kakarshin Ikon Kurdawa Labarai
  • NAHCON Tafara Shirye-Shiryen Aikin Hajjin 2026 Najeriya
  • Amurka Ta Kama Tsohon Ministan Kudin Kasar Ghana Afrika
  • Gobara Ta Tashi A Makarantar Koyon Jinyar Dabbobi Dake Jihar Kano Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.