Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Da Kuri’u Miliyan 11
Published: May 25, 2026 at 7:07 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC bayan da ya samu jimillar kuri’u miliyan 10,999,162 a sakamakon zaɓen fidda gwani da aka tattara daga faɗin ƙasar nan, inda ya yi alƙawarin ci gaba da ƙarfafa gyaran tattalin arziƙi, tabbatar da ci gaba da kuma gina tubalin sabuwar Najeriya idan aka sake zaɓensa karo na biyu.

Shugaban ya bayyana haka ne bayan karɓar takardar shaidar nasara da kuma tutar jam’iyyar APC daga hannun shugaban jam’iyyar, Farfesa Nentawe Yilwatda, a matsayin wanda zai jagoranci jam’iyyar a babban zaɓe mai zuwa.

Da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a cibiyar taro ta International Conference Centre da ke Abuja, Shugaba Tinubu ya bayyana amincewarsa da takarar cikin tawali’u da godiya ga membobin jam’iyyar.

“Yayin da nake karɓar wannan takara, ina sabunta ƙudirina na yi wa ƙasarmu hidima da ƙarin himma da jajircewa.

“Da karin shekaru huɗu na mayar da hankali da haɗin kan ƙasa, za mu tabbatar da ɗora Najeriya a kan tafarkin bunƙasar tattalin arziƙi mai ɗorewa, masana’antu, tsaron makamashi, bunƙasa ababen more rayuwa, wadatar abinci da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya,” in ji Shugaba Tinubu.

Shugaban Kwamitin Zaɓen Fidda Gwanin Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Anyim Pius Anyim, ne ya sanar da sakamakon zaɓen a wajen taron da ya samu halartar ‘yan majalisar dokoki ta ƙasa, gwamnoni masu ci da waɗanda suka yi ritaya, ministoci, masu bai wa shugaban ƙasa shawara, jiga-jigan jam’iyya da membobin kwamitin gudanarwa na APC.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na biyu, Stanley Osifo, ya samu kuri’u 16,503.

Sanata Anyim ya ce an gudanar da zaɓen ne bisa tanade-tanaden Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), dokokin zaɓe da kundin tsarin mulkin APC, inda aka gudanar da zaɓen a jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja, ƙananan hukumomi 774 da kuma mazabu 8,809 a ranar Asabar 23 ga Mayu, 2026.

Ya ce an tattara da ƙididdige kuri’un ne a Abuja ta hannun jami’an tattara sakamako, yawancinsu gwamnoni daga jihohi daban-daban.

A cewarsa, an yi wa membobin jam’iyyar miliyan 12,643,316 rajista, daga ciki miliyan 11,069,746 aka tantance, yayin da mutane miliyan 11,015,665 suka kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa.

Ya ƙara da cewa tsarin zaɓen ya kasance cikin gaskiya da adalci, inda aka bai wa wakilan ‘yan takarar damar ƙalubalantar sakamakon tare da neman gyara idan akwai buƙata.

Shugaba Tinubu ya gode wa gwamnoni, ‘yan majalisar dokoki ta ƙasa, kwamitin zaɓen fidda gwani, kwamitin gudanarwa na APC da membobin jam’iyyar bisa sake ba shi damar jagorantar jam’iyyar a babban zaɓen shekara mai zuwa.

Shugaban ya ce gwamnatinsa ta samu nasarori masu yawa a cikin shekaru uku da suka gabata, tare da kira ga membobin jam’iyyar da su yi alfahari da nasarorin APC tun daga shekarar 2015, musamman a cikin shekaru ukun baya-bayan nan.

“Tattalin arziƙinmu ya samu manyan gyare-gyare tare da sababbin dokokin haraji da manufofin kuɗi da suka ƙara yawan kuɗaɗen shiga ga tarayya.

“Mun yi alƙawarin cire matsalolin kuɗin karatu ga matasanmu. Yanzu haka mun kafa Asusun Bayar da Lamunin Karatu na Najeriya (NELFUND), inda aka riga aka raba sama da naira biliyan 282 ga fiye da mutane miliyan 1.5.

“Mun yi alƙawarin inganta samar da wutar lantarki da kawo ƙarshen tsarin lissafin kuɗin wuta na zato-zato. A cikin shekaru uku da suka gabata, mun samar da mitoci miliyan 2.5 ta hanyar shirin Presidential Metering Initiative.

“Mun kuma kafa shirin bashi na naira tiriliyan 4 domin biyan tsofaffin basussuka da ake bin kamfanonin samar da wuta da iskar gas. A ƙarƙashin gwamnatimmu, samar da wutar lantarki ya kai megawatt 6000 a wasu lokuta, wanda ya fi abin da muka gada da kashi 50 cikin ɗari.

“Mun kauce wa almubazzarancin tallafin mai, rashin daidaiton canjin kuɗi da kuma raunin ababen more rayuwa. Yanzu muna ganin sauyi: naira tana ƙara ƙarfi, ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje na ƙaruwa, kuma hasashen tattalin arziƙinmu yana da kyau duk da matsin hauhawar farashi sakamakon yaƙin Iran da rikicin Gabas ta Tsakiya.”

Shugaban ya ce gwamnatinsa ta bai wa ababen more rayuwa muhimmanci a fannoni kamar sufuri, wutar lantarki, sadarwar zamani, gidaje da ban ruwa domin samar da ci gaba mai anfani ga kowa.

“Muna gina manyan tituna masu ɗorewa a yankin bakin teku da kuma hanyar Sokoto zuwa Badagry waɗanda za su iya ɗorewa sama da shekaru 100. Muna gyara filayen jiragen sama da tashoshin jiragen ruwa bayan shekaru masu yawa na sakaci.

“Mun sake fasalin ɓangaren mai da gas tare da jawo biliyoyin daloli na sababbin jarin da aka zuba a wani ɓangare da ya kusa durƙushewa.”

Shugaban ya kuma amince cewa har yanzu akwai ƙalubalen tsaro a wasu sassan ƙasar nan.

“Ina tabbatar muku cewa ina ɗaukar alhakin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya da muhimmanci. Ba za mu huta ba har sai mun dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kowane yanki na ƙasar nan.”

Da yake magana kan ajandarsa ta wa’adi na biyu da kuma siyasar adawa, Shugaba Tinubu ya ce:

“Manufarmu a bayyane take: Gina Najeriya inda rayuwa da dukiya za su kasance cikin tsaro, inda kasuwanci zai bunƙasa, ma’aikata za su samu albashi cikin mutunci, matasa za su samu dama, manoma za su ci gaba, kuma kowane ɗan Najeriya, ba tare da la’akari da asalinsa ba, zai iya yin babban buri kuma ya cimma nasara.

“Ga waɗanda suka bambanta da mu a siyasance, muna miƙa musu hannu domin haɗin gina ƙasa. Ga waɗanda suka saɓa da manufarmu, muna ba da damar tattaunawa da haɗin kai, muna da yakinin cewa sahihancin manufarmu da sakamakon ayyukanmu za su yi magana da kansu.

“Dimokuraɗiyya ba ta dorewa da ra’ayi ɗaya kawai ba, tana dorewa ne da bambancin ra’ayi, imani da ƙasa da kuma haɗa tunani daban-daban.”

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Tsohuwar Jarumar Kannywood Wasila Ismail Ta Rasu
Next Post: Muhimmin Sako Ga Alhazai Dake Kasar Saudiya

Karin Labarai Masu Alaka

Kasashen Yankin Gulf Sun Bukaci Amurka Takawo Karshen Iran Afrika
‘Yan Ta’adda Sun Kashe ‘Yan Sanda A Jihar Katsina Najeriya
Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Ya Zamo Khalifan Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Hare Hare A Kasar Congo Ya Jikkata Mutane Da Dama Afrika
Tabbas Atiku Abubakar Ya Karbi Katin Jam’iyyar ADC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Ana Kokarin Kawo Karshen Matsalar Kashe Matafiya A Filato Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Makiyaya Sun Shiga Matsala Sakamakon Fari A Kasar Kenya Afrika
  • Sojoji Sunkai Farmaki Gidan Dan Adawa A Kasar Uganda Bobi Wine Afrika
  • Gwamnatin Kasar Guinea Ta Soke Wasu Jam’iyyun Siyasa Afrika
  • Jami’ar Tarayya A Gombe Ta Karyata Harin ‘Yan Bindiga Najeriya
  • Gwamna Bala Kauran Bauchi Ya Koma Jam’iyar APM Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tallafa Wa ’Yan Sanda Da Motoci Afrika
  • Wikki Tourist FC: Ta Sallami ‘Yan Wasa Hudu Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.