Shugaba Tinubu ya tabbatar da naɗin shugabannin Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC)
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sake naɗa sabon kwamitin gudanarwa na Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC), biyo bayan tabbatar da su da Majalisar Dattawa ta yi a ranar 16 ga Disamba.
A cikin sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar, an bayyana cewa Dokta Mulisiu Olalekan Oseni ne sabon Shugaban Hukumar (Chairman), Dokta Oseni, wanda ya fara aiki a NERC a matsayin Kwamishina tun watan Janairun 2017, daga bisani ya riƙe muƙamin Mataimakin Shugaba, Naɗinsa a matsayin Shugaba ya fara aiki ne daga 1 ga Disamba, 2025, kuma zai ci gaba har zuwa cikar wa’adin sa na shekaru goma, kamar yadda Dokar Wutar Lantarki ta 2023 ta tanada.
Haka kuma, Dokta Yusuf Ali ya zama Mataimakin Shugaban Hukumar (Vice Chairman) kuma An fara naɗa shi a matsayin Kwamishina a watan Fabrairun 2022, kuma sabon muƙaminsa zai fara aiki daga 1 ga Disamba, 2025, har zuwa ƙarshen wa’adinsa na farko.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Nathan Rogers Shatti da Dafe Akpeneye, waɗanda dukkansu ke kan wa’adin su na biyu bayan an fara naɗa su a watan Janairun 2017, Haka kuma, Aisha Mahmud Kanti Bello na ci gaba da wa’adinta na biyu, bayan an fara naɗa ta a watan Disambar 2020.
A ɓangaren sababbin mambobi, Dokta Chidi Ike na kan wa’adinsa na farko tun bayan naɗinsa a watan Fabrairun 2022, yayin da Dokta Fouad Animashaun ya fara wa’adinsa na farko daga Disamba, 2025. Dokta Animashaun ƙwararren masani ne a fannin tattalin arzikin makamashi, kuma ya taɓa zama Babban Kwamishina kuma Shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Jihar Legas.
Shugaba Tinubu ya buƙaci mambobin kwamitin NERC da su ƙara ƙaimi wajen zurfafa sauye-sauyen da ake yi a ɓangaren wutar lantarki a Nijeriya, tare da bin tanade-tanaden Dokar Wutar Lantarki ta 2023 gaba ɗaya.


