Masu gabatar da kara a ma’aikatar shari’ar Amurka sun yi murabus ana tsaka da tashin hankali game da kisan da Jami’an shige da fice na ICE suka yi wa wata mata a jihar Minnesota.
A kalla masu gabatar da kara 6 ne suka yi murabus a jihar Minnesota, kuma masu lura da harkoki da dama a sashen manyan laifuka da kare ‘yancin dan Adam na ma’aikatar suma sun sanar da ajiye aikin su, bayan da aka shiga tashin hankali kan kashe wata mata da jami’in shige da fice ya yi a birnin Minneapolis, a cewar mutane da ke da masaniya kan abun.
Murabus din ya biyo bayan karuwar tashin hankali, kan yanke shawarar da gwamnatin Shugaba Donald Trump tayi na hana jihar shiga cikin harkar gudanar da bincike kan harbin Renee Good, wadda wani jami’in shige da fice ya harbe ta a ka har lahira.
Suma lauyoyi a sashen kare hakkin dan adam, wadanda yawanci su ke bincike kan irin wannan kisa da ya kunshi Jami’an tsaro suma an sanar ba za’a sa dasu a cikin binciken ba.


